Lokacin da Collins Odhiambo ya karɓi sakamakon sakandare, harafin D da ya kalla sai ya ji kamar karshen burinsa na zama malami.
Fiye da shekaru goma bayan haka, yana aiki a matsayin ma'aikacin jinƙai a Kudancin Sudan, kuma yanzu bai ɗauki wannan lokacin a matsayin ƙofar da aka rufe ba, sai dai a matsayin farkon wata tafiya da bai zata ba.
"Ban samu makin da nake so a jarabawar ƙarshe ba," in ji Collins a tattaunawarsa da TRT Afrika. "Na dade ina son zama malami, amma duk lokacin da na nemi aiki sai amsar ta zo ta ɓata rai."
Abin da ya faru da shi yana nuna gaskiyar abin da dubban ɗaruruwan ɗalibai ke fuskanta a duk duniya a kowace shekara. Daga cikin ɗalibai 965,000 da suka rubuta jarabawar Kenya Certificate of Secondary Education (KCSE) ta 2024, 244,563 ne kawai suka samu C+ ko sama da haka, wanda shi ne ƙa'idar farko don yawancin shirye‑shiryen digiri.
Ko a tsakanin waɗanda suka ci, dubban ɗalibai ba su nemi shiga jami'a ta tsarin Kenya Central College Placement System (KUCCPS) ba.
Daga cikin waɗanda suka yi rajista, da yawa sun sha wahala don samun gurbin saboda yawan masu neman shiga.
"Fiye da shekaru biyu bayan kammala makarantar sakandare ban san abin da zan yi ba. Ba zan iya shiga kwaleji don ci gaba da karatu ba, don haka na fara yin aikin sa kai tare da kungiyoyin ba na gwamnati. A lokacin ne na fara son aikin al'umma kuma na yanke shawarar bin shi a matsayin wata hanya ta sana'a," in ji Collins.
Sabbin damarmaki
Kenya na ƙoƙarin ƙarfafa ƙarin ɗalibai su ci gaba da karatun gaba da sakandare duk da rashin kyawun maki a sakandare.
Tsarin KUCCPS da ke raba ɗalibai zuwa jami'o'i ya sanar cewa kafin 2026, ƙimar maki mafi ƙanƙanci da za a yi la'akari da ita don ba wa ɗalibai gurbi a KMTC College of Health Sciences na iya sauka zuwa D. Manufar ita ce a ba wa ƙarin ɗalibai damar shiga fannonin da a baya ba su da damar samu.
A ƙarƙashin shirin da aka gyara, ɗalibai za su fara da takardun shaida (certificates) sannan su ci gaba zuwa difloma da ake bayarwa a cibiyoyin horon kiwon lafiya a fadin ƙasar.
A matakin takardar shaida akwai kwasa-kwasai kamar mataimakin lafiya na al'umma, gudanarwar inshorar lafiya, ajiye bayanai na lafiya da fasahar bayanai, ma'aikacin gaggawa na likita (EMT), injiniyan likita, kimiyyar abinci, likitan ƙashi da lafiyar al’umma.
Kwasakwasan difloma sun fi zurfi, sun haɗa da likitanci na asibiti da tiyata, lafiyar al'umma, lafiyar baki da fasahar hakori da sauransu.
Tun daga sanarwar, KUCCPS ta samu nasarar sanya kusan ɗalibai 310,000 a cikin jami'o'i da kwalejoji daban-daban, wanda ya haɗa da shirye‑shiryen digiri, difloma da takardun shaida.
Neman hanyarsa
Collins yana ba matasa da ba su cika ka'idar shiga jami'a ba shawara kada su yi watsi da kansu, su maida hankali kan wasu damar da za su gina ƙwarewarsu kuma su taimaka musu su cimma burinsu.
"Na gwada abubuwa da yawa, ciki har da shiga rukunin wasan kwaikwayo, aikin sa kai a cikin al'umma, da taimaka wa kungiyoyi masu zaman kansu da suka amfana daga sanina unguwarmu da matasan gari.
“Na samu kwarewa a yayin aikin kuma na ƙaunaci abin da zai zama sabuwar hanyar aikina," in ji Collins ga TRT Afrika.
Kusantowa shekaru goma sha biyu tun bayan kammala sakandare, Collins ya shiga jami'a. Yana karatun digiri na farko a fannin kimiyyar zamantakewa da nazarin ci gaban al'umma, a lokaci guda yana aiki tare da NGO.
"Rashin samun maki da ka sa rai ba yana nufin ka gaza a rayuwa ba. Yana nufin kawai kana buƙatar ɗaukar wata hanya daban.
“Waɗannan hanyoyi na iya zama masu ɗimbin lada, ko ma sun fi kyau, gwargwadon sha'awarka da burinka," in ji Collins ga TRT Afrika.
A shekarar 2025, kusan ɗalibai 1,000,000 suka rubuta jarabawar Form Four ta Kenya, wacce ita ce jarabawa ta ƙarshe ta sakandare da ke yanke hukuncin shiga jami'a. Daga cikin waɗannan, ɗalibai 1,932 ne suka samu A.
Bayanai daga ma'aikatar ilimi sun nuna cewa ɗalibai 270,000 kaɗai ne suka samu C+ ko sama da haka don samun gurbin jami'a.
An shirya Collins zai kammala karatunsa a watan Agusta na wannan shekara. Ko da bai cika burinsa na zama malami ba, yana fatan tafiyarsa za ta zama shiriya ga wasu da dama da suka rasa makin da suka so samu.













