Abin da Malaman addinai suka ce kan kiran Sarkin Musulmi na daina kalaman kiyayya a Nijeriya
DUNIYA
3 MINTI KARATU
Abin da Malaman addinai suka ce kan kiran Sarkin Musulmi na daina kalaman kiyayya a NijeriyaDuka malaman bangarorin biyu na Musulmai da Kirista sun jaddada cewa akwai bukatar a rika amfani da mumbarin wajen yada manufofin adalci da girmama juna da zaman lafiya.
Sarkin Musulmai ya ce akwai bukatar CAN da ta NSCIA su yi aiki tare don tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya / Hoto: AFP / AFP

Daga Mazhun Idris

Malaman addinai a Nijeriya sun yi maraba da kalaman Sarkin Musulman kasar Muhammad Sa’ad Abubakar III cewa a guji mayar da mumbari wajen yada kalaman siyasa da ka iya sanya kiyayya a zuciyar mabiya.

A sakonsa na taya al'ummar Kiristocin kasar bikin Easter a ranar Litinin Sarkin Musulmin ya nemi hadin kan shugaban Kungiyar Kiristocin Nijeriya, CAN, Daniel Okoh, don kira ga malaman addinai da su kaurace wa kalaman siyasa a wuraren ibada.

“A matsayinmu na al'umma daya da muka hadu ta wajen babanmu Annabi Ibrahim, abubuwan da ke faruwa na al'amuran siyasa a baya bayan nan a kasarmu abar sonmu na yi wa al'ummominmu barazana sosai," in ji Sarkin Musulmin.

Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda shi ne shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci a Nijeriya NSCIA, ya ce akwai bukatar Kungiyar CAN da ta NSCIA su yi aiki tare don tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya.

Me malaman addinai suka ce?

Rabaran Joseph Hayab, Shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN reshen jihar Kaduna, ya shaida wa TRT Afrika cewa wannan kira ya zo a daidai, "duba da yadda lamuran masu wa’azi a majami’u da masallatai suke janyo ce-ce-ku-ce."

Rabaran Hayab ya ce, “Ina zaton Sultan ya yi wannan kira ne sakamakon karuwar zaman dar-dar a kasar kafin da kuma bayan zabukan da suka gabata, inda wasu limaman suka yi amfani da mumbarinsu wajen tallata ‘yan takara”.

A nasa bangaren Sheik Muhammad Bin Uthman, babban limamin Masallacin Sahaba da ke Kano ya ce, “Amfani da mumbari a wasu lokutan ka iya nufin yada zantukan kage da cin zarafi. To ya kamata a jawo hankalin irin limaman da ke yin haka.”

“Sai dai kuma kasancewar akwai malamai ‘yan siyasa, tun da har gwamna an samu wanda limami ne a wajen ibada a Nijeriya, zai yi wuya a raba irin wadannan malamai da yin sharhi kan matsalar al’ummarsu da ta shafi siyasa yayin da suke wa'azi," kamar yadda malamin ya gaya wa TRT Afrika.

"Amma dai maganar kiyayya kwata-kwata bai dace a kawo ta kan mumbari ba”.

Shi ma Rabaran Hayab ya jaddada cewa, “Babu batun kalaman kiyayya a littafi mai tsarki na Baibul.

"Yesu ya yi kira ga sahabbansa da cewa duk wanda ya ce wa dan uwansa ‘wawa’, to za a yi masa hisabi”.

Duka malaman biyu sun jaddada cewa akwai bukatar a yi amfani da mumbari wajen yada manufofin adalci da girmama juna da zaman lafiya.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Erdogan ya ce halartar shugabannin duniya COP31 zai ƙarfafa yarjejeniyar Paris kan sauyin yanayi
Emine Erdogan ta ƙaddamar da ƙungiyar ƙawance ta duniya don bunƙasa hanyoyin kawar da shara
Fiye da kashi 60 cikin 100 na mata sojojin Jamus sun ce an taɓa cin zarafinsu ta fuskar lalata
Mafi yawan ’yan Birtaniya na kallon Isra’ila a matsayin babbar barazana ga zaman lafiyar duniya
Guterres na MƊD ya yaba wa yadda Turkiyya ta shirya taron COP31
Amurka ta kwashe jiragen soji daga sansanin sama na biyu a Birtaniya bayan rahoton barazanar Iran
Ƙungiyoyin ƙwadago da na ɗalibai na shirin gudanar da sabuwar zanga-zanga a Faransa
Shin Turai za ta kare ICC, ko kuwa za ta ci gaba da neman yardar Amurka?
Trump na so a kawo ƙarshen yaƙin Iran ta diflomasiyya, Netanyahu ya ce a kai ƙarin hare-hare: rahoto
Akalla 'yan Uganda 27 sun halaka ko an yanke hukuncin sun halaka a yakin Rasha da Ukraine
Hukumomin Faransa sun kama mutum 135 da ƙara dokar hana fita a wasu birane saboda zanga-zanga
Ba makawar yin Yaƙin Duniya na III in ji tsohon shugaban Serbia
Rubio ya ce taron shugabannin Amurka, Rasha da China zai amfani duniya sosai
Faransa ta hana fita a sassan Paris yayin da zanga-zangar tsadar rayuwa ta haddasa tashin hankali
Trump ya ce Qatar ta yi tayin ba shi kyautar jirgin sama samfurin 747 bayan ya nemi a ba shi aro
Gwamnatin Trump na binciken Ilhan Omar, za ta ƙwace takardarta ta ‘yar ƙasa tare da korar ta: Rahoto
An cire wani sashe na huhun Fafaroma Leo bayan yi masa tiyatar kansa - Fadar Batikan
Koriya ta Arewa ta 'harba makamai masu linzami da dama cikin tekun Japan'
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Faransa ta ce za ta bai wa Saudiyya kariya a ɓangaren man fetur ɗinta