| Hausa
KASUWANCI
2 MINTI KARATU
Hotunan zanga-zangar ma’aikatan filin jiragen  saman Legas
Ma'aikatan filayen jiragen saman Nijeriya sun soma yajin aikin gargadi ranar Litinin don tilasta wa gwamnatin kasar inganta albashi da yanayin aikinsu.
Hotunan zanga-zangar ma’aikatan filin jiragen  saman Legas
Kungiyoyin kwadagon sun toshe hanyoyin shiga filin jiragen saman Legas da ke kudancin Nijeriya, suna neman a kyautata  yanayin aikinsu tare da inganta albashinsu/Hoto TRT Afrika Hausa / Others
17 Afrilu 2023

Ma’aikatan sun hana motoci shiga filin jiragen sama na Mohammed Murtala da ke birnin Legas.

Zanga-zangar, wadda gamayyar kungiyoyin kwadago na fannin sufurin sama ta gudanar, wani bangare ne na yajin aikin kwana biyu da suke yi.

Ma’aikatan sun tare kofar shiga filin jiragen saman da ke unguwar Ikeja, lamarin da ya sa matafiya suka yi ta takawa zuwa filin jiragen saman don motoci ba za su iya shiga ba.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda