| Hausa
KASUWANCI
2 MINTI KARATU
Ghana da China sun yi cinikayyar sama da $10bn a shekara guda
Kasar China ta ce Ghana ce har yanzu a gaba daga cikin kasashen Afirka da ke kasuwanci da ita.
Ghana da China sun yi cinikayyar sama da $10bn a shekara guda
Ghana ta zuba jari a bangarori da dama a Ghana. Hoto/AA / Others
19 Yuli 2023

Jakadadan China a kasar Ghana ya bayyana cewa kasar ta Ghana har yanzu ita ce kasar Afirka da ta fi kasuwanci da China.

Kamfanin dillancin labarai na Ghana ya rawaito Ambasada Lu Kun yana bayyana cewa adadin cinikayyar da kasashen biyu ke yi a duk shekara yana karuwa da kashi 7.3 cikin 100, inda ya ce kudin cinikayyar kasashen ya kai dala biliyan 10.

Mista Lu ya bayyana wadannan bayanai a lokacin bayar da kayan agaji da suka kai dala 50,000 ga wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su a yankin Volta.

Ya jaddada cewa gwamnatin China za ta ci gaba da iya bakin kokarinta wurin habaka tattalin arzikin Ghana.

Kasar China dai ta zuba jari a bangarori da dama a Ghana da suka hada da jirgin sama da makamashi da karafa da siminti wadanda duk sun taimaka wurin samar da ayyukan yi, kamar yadda Mista Lu ya bayyana.

Haka kuma ya ce China ta taimaka wa kwalejojin kimiyya da fasaha da na koyon sana’o’i.

MAJIYA:TRT Afrika