| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Kada ku wallafa sakon taya ni murna a jaridu: Kashim Shettima
Sanata Shettima ya yi kira ga masu son yi masa murna da su yi amfani da kudin wajen bayar da gudunmawa ga kungiyoyin bayar da agaji don su taimaka wa jama’a.
Kada ku wallafa sakon taya ni murna a jaridu: Kashim Shettima
An haifi Sanata Shettima ranar 2 ga watan Satumba na shekarar 1966,/Hoto:  Kashim Shettima/Facebook / Others
1 Satumba 2023

Mataimakin shugaban Nijeriya Sanata Kashim Shettima ya bukaci mutane su guji wallafa sakon taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa a jaridu.

Ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ranar Alhamis.

An haifi Sanata Shettima ranar 2 ga watan Satumba na shekarar 1966 don haka ranar Asabar yake cika shekara 57 a duniya.

Bisa al’ada dai, ‘yan Nijeriya da sauran mutane kamun-kafa kan biya miliyoyin kudi ga jaridu don wallafa sakonnin taya murna ga shugabanni a irin wadannan lokuta.

Sai dai Sanata Shettima ya “ina matukar godiya bisa sakonnin taya murna da mutane da dama daga cikinku” suka aiko a irin wannan rana a shekarun da suka wuce.

Amma a wannan karon, mataimakin shugaban kasar ya ce “Ina kira a gare ku da ku guji wallafa sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwata a jaridu” saboda mawuyacin halin da ake ciki a Nijeriya.

Ya yi kira ga masu son yi masa murna da su yi amfani da kudin wajen bayar da gudunmawa ga kungiyoyin bayar da agaji don su taimaka wa jama’a.

MAJIYA:TRT Afrika