Hukumomi a Nijeriya sun ce an kuɓutar da matasa 20 da ke shirin soma aikin yi wa ƙasa ƙasa hidima (NYSC) da wani mutum ɗaya da ‘yanbindiga suka yi garkuwa da su a jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin ƙasar.
An ceto mutanen ne daga dajin Amakohia-Ubi da ke ƙaramar hukumar Owerri West, bayan wani samame na haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka gudanar, in ji kakakin rundunar ‘yansandan Nijeriya, Ani Iniedu.
Tuni aka kai su asibitin Hukumar DSS da ke Owerri domin duba lafiyarsu da ba su kulawar da ta dace.
Daraktan Janar na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu, ya ziyarci waɗanda aka ceto a asibitin, tare da Kwamishinan ’Yansandan Jihar Imo, da daraktan Hukumar DSS na jihar da kuma kwamandan rundunar sojin 34 Artillery Brigade.
An sace mutanen ne a ranar 1 ga watan Oktoba, yayin da suke tafiya daga Ibadan da ke kudu maso yammacin Nijeriya zuwa sansanonin horas da matasa na NYSC a jihohin Abia da Akwa Ibom.

Daga bisani ’yansanda sun gano sansanin masu garkuwa da mutanen ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa, amma suka ce ba za su iya shiga yankin nan-take ba saboda zargin cewa an dasa bama-bamai a wurin.
Jami’an tsaro sun ƙara tura kayan aiki da suka haɗa da buldoza da motocin sulke domin sauƙaƙa aikin ceto.
A baya, rahotanni sun bayyana cewa ’yansanda sun tabbatar da ceto mutane 10 daga cikin waɗanda aka sace, yayin da ake ci gaba da neman sauran.
Haka kuma rahotannin sun ce masu garkuwa da mutanen sun nemi kuɗin fansa na naira miliyan 50 kan kowane mutum.
’Yansanda sun ce ana ci gaba da bincike domin kama waɗanda ke da hannu a garkuwa da mutanen, sai dai kawo yanzu ba a bayyana ko an kama wani ko kuma an biya kuɗin fansa ba.



















