| Hausa
DUNIYA
2 MINTI KARATU
Isra'ila ta kashe Falasdinawa 165 daga Juma'a zuwa Asabar
Tsawon kwanaki 106, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 24,762 da raunata mutum 62,108.
Isra'ila ta kashe Falasdinawa 165 daga Juma'a zuwa Asabar
Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a cikin Gaza inda take kashe mazauna birnin akasari yara kanana da mata. / Hoto: AA / AA
20 Janairu 2024

1108 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 165 daga Juma'a zuwa Asabar

Akalla Falasdinawa 165 Isra’ila ta kashe tare da raunata 280 a sa’o’i 24 da suka wuce, haka kuma akwai mutane da dama da suka makale a karkashin baraguzai sakamakon hare-hare da Isra’ila ta kai kan gidajen jama’a, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya da ke Gaza ta tabbatar.

“Ƴan Isra’ila masu mamaya sun yi kisan kiyashi ga iyalai 14 a Zirin Gaza, inda suka kashe mutum 165 da raunata 280 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata,” in ji ma’aikatar a wata sanarwa.

“Akwai mutane da dama da suka makale a karkashin baraguzai da kan tituna sakamakon masu aikin ceto sun kasa kaiwa a gare su,” in ji sanarwar.

0902 GMT — Isra'ila ta kashe farar hula bakwai a Gaza da Khan Younis

Isra’ila ta kashe farar hula akalla bakwai a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza da kuma unguwar Al Amal da ke Khan Younis, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na WAFA ya ruwaito.

Jiragen yakin Isra’ila sun kai hari wani gida mallakar iyalan Darwish a sansanin, wanda hakan ya jawo kisan farar hula biyar a sansanin da kuma raunata wasu da dama.

Haka kuma jiragen yakin na Isra’ila sun kaddamar da hare-hare da dama a unguwar Al Amal inda suka kashe akalla mutum biyu da kuma raunata wasu da dama.

MAJIYA:AA, AFP, AP, Reuters