| Hausa
DUNIYA
2 MINTI KARATU
Erdogan abokina ne kuma mutumin da nake girmamawa  — Trump
Idan kuka dubi abin da ya faru a Siriya, an raunana Rasha, an raunana Iran. Mutum ne mai dabara,” a cewar Trump dangane da Erdogan.
Erdogan abokina ne kuma mutumin da nake girmamawa  — Trump
Goyon bayan Washigton ga ƙawancen ‘yan tawayen SDF a Siriya da YPG ta mamaye na daga manyan abubuwan da ke haifar da saɓani tsakanin Turkiyya da Amurka. / Hoto: AP / Others
8 Janairu 2025

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya jaddada cewa Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan “abokinsa” ne da yake girmamawa.

Kalaman nasa sun zo ne yayin wani taron manema labarai a gidansa na Mar-a-Lago a Florida ranar Talata, lokacin da aka tambaye shi dangane da yiwuwar janye sojojin Amurka daga Siriya idan ya karɓi mulki nan gaba a wannan watan.

“Ba zan ce muku haka ba saboda wannan tsari ne na sojoji, sai dai zan ce Turkiyya ce,” a cewar Trump. “Shugaba Erdogan abokina ne, mutum ne da nake so, nake girmamawa. Ina ji shi ma yana girmama ni."

“Amma idan kuka dubi abin da ya faru a Siriya, an raunana Rasha, an raunana Iran. Mutum ne mai dabara, ya tura mutanensa ƙasar ta hanyoyi daban-daban da sunaye daban-daban, kuma sun je sun ƙwace ta,” kamar yadda Trump ya fada.

Gwamnatin Bashar al Assad ta faɗi a watan jiya bayan gamayyar dakarun hamayya sun ƙwace manyan biranen Siriya.

Miliyoyin ‘yan Siriya ciki har da jagororin hamayya, sun koma Turkiyya don tsere wa azabtarwar gwamnatin Assad. Wasunsu a yanzu sun koma don taimakawa a ciyar da ƙasar wacce yaƙi ya ɗaiɗaita gaba.

Amurka tana da sojojin kusan 2,000 a Siriya, inda Washingoton ta jima tana ƙoƙarin halasta kasancewar ƙungiyar ta’addanci ta PPK da takwararta ta Siriya YPG da sunan yaƙar Daesh.

Goyon bayan Washigton ga ƙawancen ‘yan tawayen SDF a Siriya da YPG ta mamaye na daga manyan abubuwan da ke haifar da saɓani tsakanin Turkiyya da Amurka.

MAJIYA:TRT World