AFIRKA
2 MINTI KARATU
'Yan Boko Haram sun kashe manoma da dama a jihar Borno
A ƙalla manoma 40 'yan Boko Haram suka kashe a Arewa maso-gabashin Nijeriya, in ji wani babban jami'in gwamnati.
'Yan Boko Haram sun kashe manoma da dama a jihar Borno
Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno.
13 Janairu 2025

A kalla mutane 40 'yan ta'addan Boko Haram suka kashe a jihar Borno da ke Arewa maso-gabashin Nijeriya, in ji wani babban jami'in gwamnatin jihar a ranar Litinin.

Ana zargin wani ɓangare da ya ɓalle daga ƙungiyar ta Boko Haram da ke biyayya ga 'yan ƙungiyar ISne ya kai harin a ranar Lahadin da ta gabata a garin Dumba na jihar Borno, in ji gwamnan jihar Babagana Umara Zulum.

Gwamnan ya gargaɗi fararen hula da su kasance a yankunan da suke da tsaro inda sojoji suka fatattaki 'yan ta'adda da ɓata gari daga cikin su, inda ya kuma yi kira ga jami'an soji da su gudanar da bincike game da harin.

"Ina son na tabbatar wa 'yan jihar Borno cewa za a binciki wannan batu sosai tare da ɗaukar matakan da suka kamata. Ina son amfani da wannan dama na yi kira ga rundunar soji da ta kamo tare da hukunta wadanda suka kai harin mai muni kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba," in ji shi.

Ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram mai iƙirarin jihadi a Nijeriya, sun ɗauki makamai a 2009 don yaƙi da gwamnati da kuma neman aiwatar da shari'ar Musulunci. Rikicin ya zama mafi daɗe wa a tarihin Afirka, wanda ya tsallaka zuwa maƙotan Nijeriya ta iyakar arewacin ƙasar.

Majalisar DInkin Duniya ta bayyana cewa tun daga 2014 zuwa yanzu an kashe fararen hula kimanin 35,000 a arewa maso-gabashin Nijeriya.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Sojojin Sudan sun harbo jirgi maras matuƙi na RSF a Kordofan ta Arewa
Dakarun Nijar sun cafke muggan makamai da aka yi safararsu daga Libya, sun kama masu safarar ƙwayoyi
RSF ta Sudan ta kai hare-hare a Jihar Khartoum da birnin Atbara bayan amincewa da tsagaita wuta
Paul Biya na Kamaru: Shugaban da ya fi tsufa a duniya ya sha rantsuwar kama aiki karo na takwas
Hatsarin mota ya yi ajalin fiye da mutum 1,000 a Nijar a shekarar 2023, fiye da 12,000 sun jikkata
Sabbin hotunan tauraron dan'adam sun gano alamun 'kaburburan bai-daya a El-Fasher a Sudan
MDD ta yi gargaɗin cewa yaƙin Sudan na gurgunta tattalin arzikin Sudan ta Kudu
Trump ya ce bai kamata Afirka ta Kudu ta kasance cikin G20 ba, ba zai je taronta a Johannesburg ba
'Yan Sudan sun ba da mummunan labarin yi wa mata fyade yayin da suke tserewa daga Al Fasher
An kashe mutane 40 a harin da aka kai wa taron jana'iza a yankin Kordofan na Sudan: MDD
Yadda biranen Afirka mafiya tsafta suke bayyana sauyin da ake samu a nahiyar
Sojojin Ruwa na Ghana sun kama ‘yan Nijeriya 10 da suka ɓuya a jirgin ruwan Panama a Tema
Harin jirgin sama maras matuƙi na RSF ya kashe mutane da dama a lardin Kordofan na Arewa a Sudan
Fiye da mutum 1,500 sun rasa matsugunansu a Sudan sakamakon taɓarɓarewar tsaro: MDD
Dakarun RSF sun kashe mata 300, sun yi wa 25 fyaɗe cikin awa 48 a Al Fasher – Minista
Amurka ta buƙaci a tattauna domin kawo ƙarshen yaƙin Sudan, ba amfani da ƙarfin soja ba
Ana fargabar dubban mutane na cikin 'mummunan hatsari' a birnin Al Fasher na Sudan da RSF ta ƙwace
Shugabar Tanzania Samia Hassan ta lashe zaɓen ƙasar da kashi 97.66 cikin 100
Tchiroma Bakary: Sojojin Kamaru sun yi wa jagoran 'yan adawar kasar rakiya zuwa wuri mai 'aminci'
Kudirin 1325 ya cika shekara 25: Me ya sa dole Afirka ta jagoranci samar da zaman lafiya a duniya