Wani ɗan-ƙunar-baƙin-wake ya kai hari kan wani sansanin soja a arewa-maso gabashin Nijeriya, kusa da kan iyakar ƙasar da Kamaru, inda akalla sojoji biyar suka rasa rayukansu, in ji jami'an tsaro da wasu majiyoyin yankin.
An kai harin ne kan sansanin soja a Firgi, kusa da garin Pulka a jihar Borno a ranar Lahadi, in ji majiyoyi a safiyar Talata.
‘Yanta'adda sun ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare a kan sansanonin soja a arewa-maso gabas a wannan shekara.
Umar Sa'idu, wani mamba na al'umma, ya ce mutane biyar sun mutu nan da nan bayan harin.
An harbe maharin, in ji rundunar soja.
“Bayan wasu sa'o'i, ma'aikatan lafiya a UMTH (Cibiyar Koyarwar Asibitin Jami'ar Maiduguri) sun tabbatar cewa dukkan wadanda muka ba su ‘yan rakiya, guda biyar, sun mutu,” in ji shi ta waya.
Laftanal Kanal Sani Uba, kakakin rundunar soja a arewa-maso gabas, ya tabbatar da harin.
“Sojojinmu jarumai sun harbe maharin lokacin da ya yi ƙoƙarin tayar da bam a matsugunansu,” in ji Uba.
“Abin takaici, sojojinmu jarumai sun ji rauni iri-iri kuma yanzu suna karɓar kulawar lafiya.”
Fashewar bam
Sa'idu ya ce ana zargin mai kai harin ɗan Boko Haram ne wanda ake tunanin ya fito daga tsaunukan Mandara da ke kusa da wajen.
A cewar Bukar Aji, wani mafarauci na yankin, maharin ya kusanci sojojin sai ya kunna dintayar da bam da yake ɗaure a jikinsa.
‘Yansanda sun tabbatar da harin, amma ba su bayar da cikakkun bayanai ba.
Pulka na kusa da tsaunukan Mandara, wani yanki na kan iyaka da ke tsakanin Nijeriya da Kamaru.
Wasu hare-haren masu muni
Mummunan harin ƙunar-baƙin-wake na karshe a Nijeriya ya faru ne a watan Yuni lokacin da wata mata da ake zargin tana aiki ne don Boko Haram ta kashe jami'an yaki da ta'addanci 20 a jihar Borno.
A watan Janairu, an kashe akalla sojoji 27 a wata fashewar ta'addanci a hamadar da ke kan iyaka tsakanin jihohin Borno da Yobe; wanda ya zama ɗaya daga cikin munanan hare-haren kai da aka kai kan sojojin Nijeriya a 'yan shekarun nan.















