Sakon Turkiyya kan Gaza a wani ɓangare na taron Majalisar Dinkin Duniya a ƙarshen watan Satumba ya bar shugaban Amurka Donald Trump cikin tunani, in ji Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
"A yayin taron Majalisar Dinkin Duniya, a ganawar da muka yi da Trump, mun bayyana sakonmu musamman daga ƙasashen Musulmi, kuma a matsayinmu na Turkiyya, wanda ya bar Trump cikin nazari," in ji Shugaba Erdogan a yayin ganawarwa da daliban wata jami'a a Istanbul ranar Lahadi.
"Za mu ci gaba da bin hanyarmu tare da jajircewa a lokutan da ke tafe. Babu wani koma baya. Idan muka ja da baya, ba za mu iya yin bayani a gaban Allah ko a gaban Gaza ba," in ji shi.
Kan batun Gaza kuwa, Ankara tana "ɗaukar kowane mataki", in ji Erdogan, inda ya yi waiwaye kan jawabin da ya gabatar a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a gaban dukkan wakilan.
"Wakilan Isra'ila suna zaune a gaban teburin da ke gabana. Na gabatar da wannan jawabin yayin da nake kallonsu kai tsaye. Mu ba matsorata ba ne," in ji shi.
Da yake bayyana ƙudurin Ankara kan batun Gaza, ya yi alƙawarin cewa babu guda ba ja da baya kan matsayar.
Erdogan ya ƙara da cewa, Turkiyya na da matsayi na musamman a duniya, inda ta bayyana cewa Ankara za ta karɓi baƙuncin taron shugabannin NATO.
"A baya mun taba karɓar baƙuncin taron a Istanbul, kuma yanzu za mu karɓi baƙuncin wannan taron a Ankara. Tabbas, a Ankara, mun shirya kafa tarihi."


















