KASUWANCI
2 minti karatu
Kamfanonin haɗin gwiwa ƙarƙashin Saudiyya za su sayi kamfanin wasannin game na Electronic Arts (EA)
Kamfanin EA ya shahara wurin shirya wasannin game ɗin talabijin daga ciki har da na ƙwallon ƙafar FIFA inda ake sa ran sayen shi a kan dala biliyan 55.
Kamfanonin haɗin gwiwa ƙarƙashin Saudiyya za su sayi kamfanin wasannin game na Electronic Arts (EA)
Ana sa ran kammala cinikin a farkon shekarar 2026, wanda zai buƙaci amincewar masu hannun jari na EA da hukumomin kula da harkokin kasuwanci. / AP
29 Satumba 2025

Kamfanin bidiyo na Electronic Arts (EA) ya sanar da cewa wasu kamfanonin haɗin gwiwa ƙarƙashin Asusun Zuba Hannun Jari na Saudiyya za su saye shi a kan dala biliyan 55, wanda EA ya bayyana a matsayin mafi girman cinikin hannun jari da aka biya lakadan a tarihi

Kamfanonin haɗin gwiwar sun haɗa da kamfanonin saka jari na Amurka wato Silver Lake da Affinity Partners, tare da kamfanin da Jared Kushner ya kafa a Miami, wanda shi ne tsohon mai ba da shawara a Fadar White House kuma surukin Shugaban Amurka Donald Trump.

EA, wanda aka fi sani da wasannin da suka haɗa da FIFA, Madden NFL, The Sims da Battlefield, ya bayyana samun kuɗaɗen shiga na dala biliyan 7.5 a cikin shekara guda a kwanakin baya.

Ana sa ran kammala cinikin a farkon shekarar 2026, wanda zai buƙaci amincewar masu hannun jari na EA da hukumomin kula da harkokin kasuwanci.

Asusun Zuba Hannun Jari na Saudiyya PIF, wanda tuni yake da kaso 9.9 cikin ɗari na hannun jarin EA, zai haɗa wannan hannun jarin nasa a cikin yarjejeniyar.

Za a biya cinikin ta hanyar dala biliyan 36 daga hannun jari na mambobin ƙungiyar da kuma dala biliyan 20 na bashi daga JPMorgan Chase.

Bayan kammala cinikin, za a cire EA daga kasuwar hannun jari ta Nasdaq, kuma za ta ci gaba da kasancewa a hedikwatarta da ke Redwood City, California, ƙarƙashin jagorancin Wilson.

Wannan yarjejeniya ta nuna sabon babban saka jari na PIF a fannin game ɗin wasannin bidiyo yayin da Saudi Arabia ke ƙoƙarin faɗaɗa tattalin arzikinta fiye da dogaro da kuɗaɗen man fetur.