Gwamnatin Jihar Katsina ta umarci dukkan sarakunan gargajiya da ke faɗin jihar da su nemi izinin gwamnati kafin karɓar baƙin ƙasashen waje a fadojinsu.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al'adu na jihar, Bala Salisu Zango ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 25 ga Mayu, 2026.
A cewar sanarwar, dole ne sarakunan su nemi izini daga sassan kula da harkokin ladabi da tsare-tsaren hukuma (Protocol) da kuma harkokin majalisar zartarwa da tsaro, waɗanda ke ƙarƙashin ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha, kafin su karɓi baƙin ƙasashen waje.
Gwamnatin ta ce manufar matakin ita ce tabbatar da ingantaccen tsarin gudanarwa, tsaro da kuma bin ƙa'idojin hukuma yayin ziyartar fadojin sarakunan gargajiya da baƙin ƙasashen waje ke yi.
Ta ƙara da cewa matakin zai sanya cibiyoyin sarautun gargajiya cikin wani tsari na musamman da zai kula da hulɗar ƙasashen waje, tare da tabbatar da cewa gwamnati na da masaniya kan duk wata hulɗa da cibiyoyin sarautun ke yi da baƙin ƙasashen waje.
Sanarwar ta bayyana matakin a matsayin wani ɓangare na babban shirin Gwamna Dikko Umaru Radda na ƙarfafa tsarin tsaro a matakin ƙananan hukumomi da al'ummomi.
Gwamnatin ta kuma jaddada cewa sarakunan gargajiya na daga cikin muhimman abokan hulɗarta wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ta ce tsarin neman izinin zai taimaka wajen rubuta bayanan dukkan ziyarce-ziyarcen ƙasashen waje zuwa yankunan sarakunan tare da tantance su ta fuskar tsaro.













