Har yanzu tsuguno ba ta ƙare ba a taƙaddamar da ake yi kan ƙasar da ta lashe kofin Afirka na AFCON 2025, duk da cewa ranar Talata Kotun Wasanni ta Duniya, CAS, ta yanke hukuncin tabbatar wa Senegal lashe kofin.
Jim kaɗan bayan fitar da hukuncin, hukumar ƙwallo ta Morocco ta fitar da sanarwa a hukumance, wadda ta yi wasu zarge-zarge, tare da shan alwashin ɗaukaka ƙara a duk matakan da suke bisa doka don ganin ta yi nasara.
Tun da fari Senegal ce ta lashe kofin bayan doke Morocco da ci 1-0, a wasan da ‘yanwasan Senegal suka ƙauracewa filin wasa na tsawon mintuna, kafin su dawo sakamakon an bai wa Morocco fenareti da suke ganin bai cancanta ba.
Watanni biyu bayan kammala gasar, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka, CAF, ta karɓe kofin daga hannun Senegal, kuma ta bai wa Morocco tare da nasarar ci 3-0, bisa zargin ‘yanwasan Senegal sun sallama wasan lokacin da suka ƙauracewa fili.
Zargin muna-muna
Senegal ta shigar da ƙara gaban Kotun Warware Taƙaddamar Wasanni ta CAS, wadda a yanzu ta yanke hukuncin tabbatar wa da Senegal nasara a gasar.
Kotun da dogara ne kan hukuncin alƙalin wasa wanda ya amince da cigaba da wasan, bayan tsaikon da ya faru.
Da take watsi da hukuncin, Morocco ta yi zargin cewa awanni 48 kafin fitar da hukuncin, wani cikin alƙalan kotu mai suna Ulrich Haas, ya yi magana ta waya da shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Senegal.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Morocco, FRMF ta kuma yi nuni da wani mataki da hukumar kula da ƙa’idojin wasannin kwallon ƙafa ta duniya IFAB, da hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA, suka ɗauka dangane da ‘yanwasan idan suka bar fili ba tare da izinin alƙali ba.
A yanzu dai, rahotanni sun ce Morocco tana da kwanaki 30 ta shigar da ƙara gaban kotun ƙoli ta Switzerland, duk da damar yin nasara za ta ƙara yi mata wahala.












