Fitaccen Jarumin fina-finan Nijeriya na Nollywood, kuma tsohon ɗanjarida Pete Edochie ya rasu yana da shekara 79, kamar yadda iyalasan suka bayyana ranar Laraba.
Wata sanarwa da ɗan marigaryin, Leo Pete Edochie, ya fitar a madadin iyalinsa, ta ce ɗanwasan kwaikwayon ya rasu ne kafin asubahin ranar 25 ga watan Nuwamban 2026 a Enugu bayan ya ɗauki lokaci yana fama da kansar mafitsara.
Iyalin sun bayyana marigayin a matsayin “mijinmu da babanmu da ɗan’uwanmu da muke so”.
“Da cikakken baƙin ciki da kuma zukata da suka miƙa wuya ga Allah maɗaukaki, muna sanarwar da rasuwar mijinmu da babanmu da ɗan’uwanmu... Cif Dr Pete EDOCHIE.., tsohon ma’aikacin rediyo da talbijin da kuma fitaccen ɗanwasan kwaikwayo,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Marigayin wanda ɗan asalin Akamnato Ifite Nteje ne a Jihar Anambra, ya rasu ya bar matarsa Josephine Edochie da ‘ya’ya da ‘yan’uwa da yawa.
Kazalika iyalinsa sun bayyana cewa za a fitar da shirin jana’iazarsa sannun a hankali.
“Yayin da muke jimamin wannan rashin mai raɗaɗi, muna addu’a Allah maɗaukaki ya jiƙansa da kuma bai wa iyalinsa haƙurin jure wannan babban rashin,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
“Alla Ya kasance tare da mu a wannan lokaci mai matuƙar wahala,” in ji sanarwar.
An haifi Edochie ne ranar 7 ga watan Maris na shekarar 1947 a Zaria, Jihar Kaduna, kuma ya kasance ɗan asalin ƙabilar Igbo.
Ya halarci makarantun Firamare na St. Patrick da St. James a Zaria sannan ya tafi makarantar St. John’s College don karatun sakandare. Daga baya ya yi karatu a makarantar Aikin Jarida da Talbijin a Ingila.
Shauƙin Edochie ga wasan kwaikwayo ya bayyana ne tun yana yaro, yayin da yake ɗalibi a makarantar sakandaren St. John College a Kaduna.
A shekarar 1962, a lokacin da yake ɗan shekara 15, ya kasance cikin ‘yanwasan kwaikwayon da suka yi wasan ‘The Merchant of Venice’ na William Shakespeare a kan dandali.
A shekarar 1967, Edochie ya fara aiki a gidan rediyo da talbijin, inda ya samu matsayin ƙaramin mataimakin mai tsara shirye-shirye da gidan Watsa Labaran Gabashin Nijeriya (ENBS), ma’aikatar da ta koma Gidan Watsa labaran Jihar Anambra (ABS).
Ya shafe shekaru yana ƙara girma har zuwa lokacin da ya kai matakin darakta.
Ya yi aiki a matsayin daraktan tsara shirye-shirye da mataimakin manajan darakta kuma a wasu lokuta ya yi aiki a matsayin muƙaddashin manajan darakta.
Aikinsa a ABS ya ƙare ne a lokacin da gwamnatin ta zaɓi shigar da siyasa cikin ayyukan tashar FM ɗinsa, wani matakin da ya sa aka buƙaci dukkan shugabannin gidan watsa labaran, ciki har da Edochie, su ja gefe.
Duk da cewa a da shi aka tsayar don ya zaman Manajin Darakta na gaba, ya bar gidan kuma ya shiga cikin harkar fina-finai.
Kafin wannan sauyin, ya riga ya samu damar aikin fim ɗinsa na farko a matsayin jarumi Okonkwo wasan talbijin na da aka yi kan littafin ‘Things Fall Apart,’ wanda aka yi a gidan Talbijin na Nijeriya (NTA) a shekarar 1987.
Edochie ya kasance ɗaya daga cikin ‘yanwasan kwaikwayon da suka fi fice a Nijeriya, inda ya shahara kan yadda yake jan hankali a fina-finai da kuma rawar da ya taka a fagen fina-finan Nollywood.












