Gwamnatin Sudan ta yi watsi da tayin Ethiopia na karɓar baƙuncin wata tattaunawar zaman lafiya da za ta haɗa dukkan ɓangarorin Sudan, tana mai nuna shakku kan rashin daidaiton Addis Ababa.
A wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran gwamnatin Sudan, SUNA, ya wallafa, gwamnatin ta ce Firayim Ministan Ethiopia, Abiy Ahmed, ya gayyaci ɓangarorin Sudan a ranar Talata domin shiga wata tattaunawa buɗaɗɗiya da za ta haɗa kowa da kowa, wadda Ethiopia za ta ɗauki nauyinta tare da karɓar baƙuncinta.
Gwamnatin Sudan ta ce, “Rashin daidaiton ƙasar da za ta karɓi baƙuncin tattaunawar da kuma mutunta ikon Sudan na cin gashin kanta na daga cikin muhimman sharuɗɗan amincewa da kowace ƙasa ta taka rawa a lamarin.”
Gwamnatin ta sake nanata zarge-zargen da take yi wa Ethiopia na cewa tana goyon bayan rundunar Rapid Support Forces (RSF), tare da cewa an kai hare-haren jirage marasa matuƙa kan Sudan daga cikin ƙasar Ethiopia.
Dangantakar tarihi
Ma’aikatar Harkokin Wajen Ethiopia ta yi kakkausar suka ga zarge-zargen, inda ta jaddada abota da kuma dangantakar tarihi tsakanin al'ummomin Ethiopia da Sudan. Ta kuma yi watsi da iƙirarin da ke danganta ƙasar da rikicin Sudan.
A ranar Talata, Abiy Ahmed ya bayyana cewa Ethiopia a shirye take ta karɓi baƙuncin tattaunawar ƙasa da za ta haɗa dukkan ɓangarorin Sudan, ciki har da ƙungiyoyin farar hula da na soji, tare da ɗaukar nauyinta.
Ya ce babban burin tattaunawar shi ne kawo ƙarshen yaƙin da kuma buɗe hanyar samar da gwamnatin haɗin kan ƙasa da za ta samu karɓuwa daga ɓangarori daban-daban.
Sai dai gwamnatin Sudan, bisa la'akari da zarge-zargen da take yi wa Ethiopia, ta ce ƙasar ba ta cika sharuddan rashin daidaito da ake buƙata domin karɓar baƙuncin tattaunawar ko ɗaukar nauyinta ba.
Ta kuma yi kira ga Ƙungiyar Tarayyar Afirka da sauran masu ruwa da tsaki na yanki da na ƙasa da ƙasa da su mutunta matsayarta, tare da cire Ethiopia daga duk wani shiri na karɓar baƙuncin tattaunawar ko ɗaukar nauyinta.
Yaƙin Sudan ya ɓarke ne tsakanin sojin ƙasar da rundunar RSF a watan Afrilun 2023, sakamakon rashin jituwa kan shirin shigar da mayaƙan RSF cikin rundunar sojin ƙasar.
Yaƙin ya yi sanadin mutuwar dubban mutane masu yawa, tare da raba miliyoyin jama'a da muhallansu, sannan ya haddasa mummunar barna, ciki har da lalata asibitoci da sauran muhimman kayayyakin kiwon lafiya.












