| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
An mayar wa Senegal kambun Zakarun Gasar AFCON ta 2025
An mayar wa Senegal kambun zakarun gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025, bayan Kotun Sasanta Rikicin Wasanni (CAS) ta amince da ƙarar da ƙasar ta ɗaukaka kan hukuncin cire mata kambun a ranar Talata.
An mayar wa Senegal kambun Zakarun Gasar AFCON ta 2025
An mayar wa Senegal kambun Zakarun Gasar AFCON ta 2025 / Reuters
 

An mayar wa Senegal kambun zakarun gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025, bayan Kotun Sasanta Rikicin Wasanni (CAS) ta amince da ƙarar da ƙasar ta ɗaukaka kan hukuncin cire mata kambun a ranar Talata.

Hukuncin kotun ya soke matakin Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) na ayyana Morocco a matsayin zakara, duk da cewa Senegal ta doke ƙasar mai masaukin baki da ci 1-0 bayan an tashi daga mintuna 90 na ainihin wasa zuwa ƙarin lokaci a wasan ƙarshe da aka buga a birnin Rabat a watan Janairu.

Rikicin ya samo asali ne bayan alkalin wasa ya ba Morocco bugun fenariti a ƙarshen lokacin wasa na yau da kullum. A matsayin nuna rashin amincewa, 'yan wasan Senegal sun fice daga filin wasa na tsawon mintuna 14, inda wasu daga cikinsu suka koma ɗakin sauya kaya kafin daga bisani su dawo domin ci gaba da wasan.

Sai dai Morocco ta kasa cin moriyar bugun fenarit ɗin, lamarin da ya sa aka tafi ƙarin lokaci. A nan ne Senegal ta zura ƙwallon da ta ba ta nasara.

Dalilin da ya sa aka cire wa Senegal kambun

Watanni biyu bayan wasan ƙarshe, kwamitin ɗaukaka ƙara na CAF ya yanke hukuncin cewa Senegal ta yi watsi da wasan ta hanyar ficewa daga filin wasa. Kwamitin ya soke sakamakon wasan, tare da bai wa Morocco nasara da ci 3-0, wanda hakan ya mayar da ita zakara.

Senegal ta garzaya kotun CAS, wadda ita ce kotu mafi girma da ke sauraron ƙararrakin da suka shafi wasanni. Ƙasar ta shigar da ƙarar ne a ranar 25 ga Maris, yayin da aka saurare ta a ranar 8 ga Oktoba.

Kwamitin alkalai uku ne ya saurari ƙarar, ƙarƙashin jagorancin ƙwararren masanin dokokin wasanni na Faransa, Gerald Simon. Sauran mambobin sun haɗa da farfesan dokokin ƙasa da ƙasa na Italiya, Luigi Fumagalli, da farfesa a fannin shari'a a Jami'ar Zurich, Ulrich Haas.

Sakataren Janar na CAS, Matthieu Reeb, ya ce kwamitin ya gano cewa alkalin wasan bai yi wani kuskure ta fuskar doka ba.

Wannan hukunci ya tabbatar da nasarar Senegal a wasan ƙarshe, tare da mayar mata da kambun zakarun gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025.