| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekara 80, ya tuna goyon bayan da ya ba shi a 2007
Tinubu ya kuma yaba wa Atiku kan gudunmawar da ya bayar a fannonin ilimi, kasuwanci da zuba jari a kamfanoni masu zaman kansu.
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekara 80, ya tuna goyon bayan da ya ba shi a 2007
Tinubu ya ce Atiku ya ba da gudunmawa wajen gina kasa / X/Bayo Onanuga
 

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya taya tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar, murnar cika shekara 80 da haihuwa, inda ya tuna goyon bayan da ya ba shi a takararsa ta neman shugabancin ƙasa a shekarar 2007.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar a ranar Laraba, 25 ga Nuwamba, Tinubu ya yaba wa Atiku bisa irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Nijeriya, musamman tsawon shekarun da ya shafe yana harkokin siyasa da jajircewarsa wajen tabbatar da dimokuraɗiyya mai bai wa jam’iyyu da ra’ayoyi daban-daban damar kasancewa.

Shugaban ya ce sun yi tarayya wajen wannan manufa ta dimokuraɗiyya, inda ya tuna goyon bayan da ya bai wa Atiku a takararsa ta neman shugabancin ƙasa a shekarar 2007, a ƙarƙashin jam’iyyar Action Congress (AC) ta wancan lokaci.

Tinubu ya ce wannan goyon baya ya samo asali ne daga imaninsa cewa dimokuraɗiyya tana bunƙasa ne idan ’yan siyasa suka samu ’yancin shiga harkokin siyasa, gabatar da manufofi daban-daban da kuma bayar da gudunmawa wajen tattaunawar ƙasa kan shugabanci da tafiyar da gwamnati.

Ya kuma jaddada matsayinsa na goyon bayan siyasa ba tare da ƙiyayya ba, yana mai cewa ya kamata a riƙa barin ƙofa a buɗe domin sulhu bayan saɓani ko rashin jituwa tsakanin ’yan siyasa.

Ya ce, “Duk da bambancin jam’iyyun siyasar da muke ciki da kuma saɓanin ra’ayoyin da kan kasance a tsakaninmu, ya kamata dimokuraɗiyyar Nijeriya ta ci gaba da amfana da ’yan ƙasa masu jajircewa wajen shiga harkokin dimokuraɗiyya, ci gaban ƙasa da kuma bin doka da oda.”

Tinubu ya kuma yaba wa Atiku kan gudunmawar da ya bayar a fannonin ilimi, kasuwanci da zuba jari a kamfanoni masu zaman kansu. Ya yi tsokaci kan kafa Jami’ar American University of Nigeria da Atiku ya yi a Yola, yana mai cewa jami’ar ta faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi mai zurfi tare da ƙarfafa bunƙasa ƙwarewar al’umma.

Shugaban ya amince cewa shi da Atiku a yanzu suna bin hanyoyin siyasa daban-daban, kuma suna da saɓanin ra’ayoyi kan wasu batutuwan ƙasa, amma ya ce ya kamata jajircewarsu ta bai ɗaya wajen tabbatar da haɗin kan Nijeriya da zaman lafiyar dimokuraɗiyya ta kasance mafi muhimmanci.

Atiku, wanda ya riƙe muƙamin mataimakin shugaban Nijeriya daga shekarar 1999 zuwa 2007, shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Tinubu ya yi masa fatan samun ƙoshin lafiya, ƙarin ƙarfi da kuma samun damar ci gaba da yi wa Nijeriya da bil’adama hidima na tsawon shekaru masu zuwa.