NIJERIYA
2 minti karatu
An kashe 'yan ta'adda fiye da 592 a Borno tun daga Maris din 2025 - Ministan Yada Labaran Nijeriya
Ministan yaɗa labarai na Nijeriya, Muhammed Idris ya ce gwamnatin Nijeriya tana yin nasara a yaƙinta da ta'addanci, inda ake samun manyan cigaba a arewa ta tsakiyar ƙasar.
An kashe 'yan ta'adda fiye da 592 a Borno tun daga Maris din 2025 - Ministan Yada Labaran Nijeriya
Ministan sadarwa na Nijeriya
4 awanni baya

Gwamnati tarayyar Nijeriya ta jaddada cewa tana yin nasara a yakinta da ta’addanci, bayan cim ma wasu manyan nasarori da ta samu a yankin arewa maso Gabashin Nijeriya.

Da yake magana a wajen wani taron manema labarai, ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris, y ace dakarun ƙasar sun kashe ‘yan ta’adda 592 a Jihar Borno, tun daga watan Maris ɗin 2025.

“A watan Maris, wani rahoto da Cibiyar Global Terrorism Index, mai tattara bayanai kan ta’addanci ta nuna cewa hare-haren ‘yan ta’adda sun ragu sosai zuwa mafi ƙanƙantar mataki a cikin shekara 10 da suka wuce a Nijeriya.

Ba gwamnatin Nijeriya ba ce ta faɗi hakan, cibiyoyin ƙasa-da-ƙasa ne suke ba da waɗannan bayanan,” in ji ministan.

“A cikin wata takwas da suka wuce, sojojin Nijeriya sun kawar da ‘yan ta’adda fiye da 592 a Jihar Borno kawai.

“An saki mutum 11,200 da aka yi garkuwa da su kuma ana ci gaba da hakan, abu mafi muhimmanci shi ne fiye da ‘yan ta’adda 124 da iyalansu sun miƙa wuya. Sun miƙa makamai fiye da 11,000 ga hukumomin tsaro.

Ajiye makamai

Ministan ya ce, gwamnati mai ci ta zuba jarin miliyoyin daloli wajen samar da kayan aiki na zamani ga hukumomin tsaro.

Ministan ya kuma ce a yankin Arewa Maso Yammacin ƙasar ma ana ci gaba da kashe miyagu. Lamarin da ya sa ‘yan bindiga ke ta miƙa wuya a yankin.

Minista Idris ya ba da misali da ƙasurguman ‘yan bindiga da hare-haren sojoji suka kashe, kamar su Ali Kawaje da aka fi sani da Ali Kachalla, wanda ya mutu a kusa da Manforo a ƙaramar hukumar Munya ta Jihar Neja.

Sai kuma ƙasurgumin ɗan ta’adda na Jihar Zamfara, wato Kachalla Halilu Sububu da yaransa 38.

“A Arewa Maso Yamma, musamman a Zamfara da Kaduna, an ceto mutum 11,250 da aka yi garkuwa da su, kuma wasu daga cikin shugabannin ‘yan ta’addar da suka gallabi rayuwar al’umma duk an kashe su.

“Dukkan waɗannan an aika su garin da ba a dawowa. Ko a watan Agustan da ya wuce kaɗai, a samame ɗaya sojoji sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 400, waɗanda suka taru don kai hari wani ƙauye a Jihar Zamfara,” in ji Ministan.