Wata hukuma mai kula da laifukan kudi na duniya a ranar Jumma'a ta cire kasashe hudu na Afirka da suka hada da Afirka ta Kudu, Nijeriya, Mozambique da Burkina Faso - daga jerin kasashen da ake sa ido akansu saboda yawan kudaden da ake safararsu ba bisa ka'ida ba.
An sanya kasashen na yankin Kudu da Hamadar Sahara masu karfin tattalin arziki a cikin jerin 'wadanda ake sa wa ido' na Financial Action Task Force (FATF) a shekarar 2023.
Mozambique ta kasance a jerin tun daga shekarar 2022, yayin da Burkina Faso ta shiga tun 2021.
Hukumar FATF da ke birnin Paris ta sanar da cire wadannan kasashe hudu daga jerin a karshen wani taron koli.
Masana sun ce cire kasashen daga wannan jerin na iya saukaka shigar jari cikin wadannan kasashe da kuma rage jinkirin mu'amalar kudi.
Hukumar FATF ta bayyana cewa Afirka ta Kudu ta inganta kayan aiki don gano safarar kudade da kuma daukar matakan hana daukar nauyin ta'addanci.
Ita kuma Nijeriya ta karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumominta, yayin da Mozambique ta inganta rabon bayanan sirri na kudi, sai Burkina Faso da ta kara sa ido kan cibiyoyin kudi da masu kula da harkokin kudi.










