TURKIYYA
3 minti karatu
Ana shirin fara taron TRT World Forum karo na 9 a Istanbul
Tun daga farkon, Taron TRT World ya zama wata babbar hanya don haɗa muryoyi daga nahihoyi da kuma kawo fahimta tsakanin ƙasashen da suka ci gaba da masu tasowa
Ana shirin fara taron TRT World Forum karo na 9 a Istanbul
Tun lokacin da aka fara, TRT World Forum ya zama wata muhimmiyar kafa don hada muryoyi daga nahiyoyi daban-daban / TRT World
30 Oktoba 2025

Za a fara taron TRT World Forum karo na tara a Istanbul a ranar Jumma’a, inda shugabanni, masana da masu son kawo sauyi a duniya za su taru daga sassa daban-daban na duniya don tattauna yadda ake sake fasalin yanayin duniya a wannan lokaci na rashin tabbas.

Taron na kwanaki biyu, wanda aka shirya a karkashin taken "Sabon Tsari na Duniya: Daga Tsohon Tsari zuwa Sabbin Abubuwa," zai bincika yadda sauye-sauyen tattalin arziki, fasaha, kafofin watsa labarai da dokokin kasa da kasa ke sake fasalin duniyar da muke rayuwa a ciki.

Taron, wanda gidan talabijin na TRT ke shiryawa, yana zama wata muhimmiyar dama don kawo batutuwan da ba a cika magana a kansu ba zuwa gaba, tare da tambayar rawar da kafofin watsa labarai ke takawa wajen tsara labarun duniya.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, zai gabatar da jawabin bude taron, wanda ya kasance al’ada tun lokacin da aka fara wannan taron a shekarar 2017.

Jawaban da ya gabatar a baya sun mayar da hankali kan rawar Turkiyya da ke takawa a harkokin ƙasa da ƙasa domin samar da tsari mai adalci a duniya.

A bana, za a tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka hada da:

  • Gina 'Yancin Tsarin Tsaro: Turkkiya da Sabon Tsarin Tsaro na Duniya

  • Farfaɗowar Syria: Taswirar Gina Sabon Tsari da Karkata Zaman Lafiya

  • Makomar Rikici: Rikici da Sulhu a Gabashin Afirka

  • Daga Zama Wanda Aka Zalunta Gwagwarma: Hanyar Adalci a Gaza

Amma tattaunawar ba ta tsaya kan siyasa da manufofi kawai ba. Taron zai kuma dauki wani muhimmin bangare na fasaha ta hanyar wani aiki na musamman daga mai aikin zayyana daga Norway, Vibeke Harper, mai taken "3,925 Makomar da Aka Rasa."

A farkon wannan watan, Harper ta gudanar da wani aikin tunawa da mutane na tsawon sa’o’i 68 a Oslo, inda mahalarta suka karanta sunayen yara 18,459 da aka kashe a Gaza, kowanne suna an rataye shi a bango a matsayin tunawa mai dorewa.

A taron TRT World Forum 2025, Harper za ta sake fasalin wannan aikin zuwa wani sabon tunawa, inda za a gayyaci mahalarta su karanta da rubuta sunayen matasa 3,925 masu shekaru 18 zuwa 20 da aka kashe a hare-haren Isra’ila — kowanne suna za a rubuta shi a kan jar takarda kuma a sanya shi a bango a matsayin nuna girmamawa cikin shiru.

Wannan aikin fasaha yana kara wani bangare mai zurfi na jin kai da motsin zuciya ga tattaunawar da ake yi a taron, yana tunatar da mahalarta cewa a bayan kowace ƙididdiga, akwai wani labari — kuma dole tattaunawa game da duniya ta kasance mai cike da tausayi kamar yadda take cike da nazari.

Tun lokacin da aka fara, TRT World Forum ya zama wata muhimmiyar kafa don hada muryoyi daga nahiyoyi daban-daban, kawo fahimta tsakanin Arewacin Duniya da Kudancin Duniya, da yin tambayoyi masu wuya game da irin duniyar da muke ginawa.