A kowane lokaci akwai ɗaruruwan manyan jiragen ruwan dakon mai da aka faka su a Tekun Fasha, suna jiran wucewa ta wata hanya tsukakkiya wadda ƙaramin jirgin ruwa mai gudu zai iya wucewa a ƙasa da awa ɗaya.
Duk da haka, ta wannan hanya mai nisan kilomita 33, ake jigilar ɗanyen mai daga Saudiyya, Iraki, Kuwait da UAE a hankali, don ciyar da kasuwannin makamashi daga Tokyo zuwa Rotterdam.
Wannan hanya, wadda aka fi sani da Strait of Hormuz wato Mashigin Hormuz, a mafi yawan ƙididdiga ita ce hanyar ruwa mafi muhimmanci a fannin tattalin arzikin duniya.
Yanzu Irn ta ce ta rufe ta, inda kuma ta yi gargaɗin cewa duk wani jirgi da ya yi ƙoƙarin ƙetarewa zai fuskanci hari.
Kasuwannin mai sun yi martani nan take, kuma dalilin ya zama a bayyane idan aka nuna ƙididdiga. Kusan ɗaya cikin biyar na man duniya na kowace rana yana wucewa ta wannan tashar.
Akwai bututun mai da aka samar don kauce wa hanyar, sai dai suna ɗaukar wani ɗan ƙaramin adadi ne kawai sannan kuma babu wata hanya a madadinta da za ta iya ɗaukar jigilar mai yawan yawan wannan.
Wannan ne abin da ya sa tashar take da matuƙar muhimmanci, in ji Klaus Jurgens, wani masani a harkokin siyasa da dabarun sadarwa.
“Ko da yake fadinta yana ƙasa da kilomita 50, tana wakiltar kusan kashi 20 cikin ɗari na kasuwancin ɗanyen mai na duniya, ko kimanin ganga miliyan 20 a rana a ƙididdigar 2024,” in ji Jurgens.
“Za a iya cewa sauran kashi 80 zai ci gaba da wanzuwa, amma dole ne mu yi la'akari da cewa duk inda aka samu ragin kashi 20 na samar da ɗanyen mai za a ga tasiri mai tsanani.”
“Kowane irin ragin zai iya haifar da ƙaruwa a farashin ga jama’a da kasuwanci da tattalin arziƙi baki ɗaya, har da wuraren da ake amfani da man wurin ɗumama gida.
Me rufe tashar ke nufi?
Masanan makamashi sun daɗe suna yin hasashen yadda za ta kasance idan aka samu matsala a Mashigin Hormuz, inda suke bayyana irin wannan yanayi da ɗaya daga cikin mafi tsananin yanayi da tattalin arziƙin duniya zai iya fuskanta.
Sakamakon farko nan take zai kasance tashin farashin mai, wanda zai bazu cikin sauri zuwa ƙarin cajin mai a jiragen sama, farashin jigila da kuma farashin kayayyaki ga masu amfani a fannoni da dama.
Kasashen kudancin duniya da kudu maso gabashin Asiya, waɗanda suka dogara sosai ga shigo da makamashi, suna iya jin tasirin farko, ko da yake ba nan kaɗai za a ga matsin lamba ba.
Tattalin arzikin masana'antu a Turai da Asiya waɗanda suka dogara da ɗanyen mai daga Gulf na iya fuskantar wani nau'i na ƙalubale: tsawon rashin tabbas wanda zai ƙara kuɗi da hana zuba jari a cikin tsarin safara.
“Hakan ya riga ya bayyana a Jamus a jiya, inda a wasu yankuna farashin fetur a tashoshin mai ya tashi kusan dala 2.20 a duk lita,” in ji Jurgens.
“ Tankokin mai da ke amfani da wannan hanya ba wai sun nufi Turai ne kaɗai ba, har ma da yadda suka nufa China da Indiya. Hakan zai shafi ƙasashen Gulf masu mai, domin wannan tashar ita ce hanyar tafiyarsu ta teku kadai. Ciki har da jigilar LNG, tare da Qatar a matsayin babbar mai samarwa; ƙasar na aika kusan duk LNG ɗinta ta wannan tashar.'
Sakamakon shi ne jerin tasiri daga ƙasashen Gulf masu samar da man fetur waɗanda ba za su iya fitar wa masu amfani da motoci da ke Jamus ko kuma kamfanonin ƙere-ƙere a Belgium, kamar yadda Jurgens ya ce, wanda ya kuma yi gargaɗin cewa hauhawar farashi shi ne babban abin da ake tsammani.
Bangaren kudi ma yana da muhimmanci. Ƙimar inshorar haɗarin yaƙi a kan manyan tankunan kasuwanci ta ƙaru kusan nan da nan bayan sanarwar Tehran.
Kamfanonin jigila ba sa yawan tura jiragensu cikin ruwan da ba za su iya tabbatar da tsaronsa ba, wanda ke nufin zirga-zirgar kasuwanci na iya ragewa ko dakatawa ko da kafin a kai hari kai tsaye.
Wannan shi ne abin da gwamnatin Trump take ƙoƙarin hamayya da shi. Shugaban ƙasa ya bayyana cewa Rundunar Sojin Ruwa ta Amurka za ta rika raka tankunan mai na kasuwanci ta wannan tashar idan ya zama dole, kuma Washington za ta ba da tabbacin inshora don taimaka wa ci gaba da jigilar Gulf duk da ƙarin haɗari.
Matakin ba kawai ƙaramin mataki na soja ba ne, har ma alamar kasuwa: yunƙurin kwantar da hankali ga kamfanonin jigila cewa hanyar za ta iya ci gaba da kasancewa a buɗe ga kasuwanci ko da tashin hankali ya ƙaru.
“Sanar da rufe tashar wani abu ne daban, kai hari ga jiragen da ke wucewa wani abu ne na daban. A gaskiya, irin waɗannan hare-hare ba zai zama dole ba. Kamfanonin inshora, sannan kuma kamfanonin jigila za su iya yanke shawarar kada su yi amfani da tashar saboda fargaba daga yiwuwar hare-hare, ko da babu wani hari da aka kai,” in ji Jurgens.
“Kudin inshora ya riga ya tashi, tare da yawancin masu inshora suna ƙin biyan kuɗin waɗanda ke son wucewa ta tashar baki ɗaya. Raka tankuna da jiragen sintiri na soja ba lallai ba ne su sa masu inshora su canza ra'ayinsu,” kamar yadda ya ƙara da cewa.
Sahale wa China
Wasu rahotanni a kafofin watsa labarai sun yadu inda suna cewa akwai yiwuwar cewa jiragen ruwa na China na iya samun izinin wucewa ba tare da fuskantar barazanar Iran ba. Tehran da Beijing ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba domin tabbatar da irin wannan shirin.
Amma idan hakan ta faru, masana suna cewa hakan zai haifar da manyan sakamako a siyasar duniya.
“Ana yawo da ikirarin cewa za a bar jiragen da suka ɗauki tutar China su wuce kawai. Ko da gaskiya ne, ya kamata a yi la’akari da wannan, domin COSCO Shipping na China ya riga ya dakatar da amfani da tashar a mafi yawan lokuta. Abin da ya fi ban sha'awa shi ne cewa China na ɗaya daga cikin manyan masu sayen mai daga Iran. A lokaci guda, kusan kashi 50 cikin ɗari na shigo da mai na China na fitowa ne daga masu samar a yankin Gulf,” in ji Jurgens.
“Saboda haka ba abin mamaki bane cewa China na matsa lamba ga Iran don ta bar tashar a buɗe, ko da hakan bai yi nasara ba a yanzu.”
“A lokaci guda, China na iya ƙara sayen mai daga Rasha, wanda hakan zai mayar da hankali kan manufofin takunkumin Amurka kan Moscow. Rikici tsakanin Washington da ƙasashen da za su sake farawa ko ƙara kasuwanci da Rasha na iya ƙaruwa.'
Beijing ta shafe shekaru tana sayen mai daga Iran, man da aka rage farashinsa saboda takunkumin Amurka data saka wa man don kada ya kai ga kasuwannin manya.
China har yanzu ita ce babbar abokiyar kasuwanci ta Iran kuma, a fannoni da dama, wanda wannan ne goyon bayan tattalin arziƙin da ta ba Tehran damar jure wa takunkumin ƙasashen Yamma.
Barin jiragen China su wuce yayin da ake barazana ga wasu na aika bayyanannen saƙo game da hangen Iran kan abokan tarayya da abokan gaba.
A wannan yanayin, China za ta iya samun fa'ida nan take. Ci gaba da samun mai daga Gulf a lokacin da abokan hamayya ke fuskantar rikici zai samar mata da mai da kuma da kuma dama ta ɓangaren farashi.
Harkokin kasuwanci na China sun fi zurfi a cikin tsarin ciniki na duniya, kuma ƙaruwar rikicin soji a Gulf zai haifar da haɗari waɗanda suka zarce kowace fa'ida ta ɗan gajeren lokaci daga mai.
















