NIJERIYA
5 minti karatu
An yi gagarumin garambawul ga rundunar sojojin ƙasa ta Nijeriya
Mai magana da yawun sojin ƙasa ta Nijeriya, Appolonia Aneke, ce ta sanar da sabbin naɗe-naɗen a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis.
An yi gagarumin garambawul ga rundunar sojojin ƙasa ta Nijeriya
Laftanar Janar Shaibu ya yi kira ga manyan hafsoshin da aka bai wa sabbin muƙaman su yi amfani da ƙwarewarsu wajen magance rashin tsaro a Nijeriya / Nigerian army
21 awanni baya

Sabon babban hafsan sojojin ƙasa na Nijeriya, Waidi Shaibu, ya sauya wa manyan hafsoshin sojin ƙasar muƙamai “domin ƙara ƙarfafa jagorori da tsarin shugabancin rundunar da kuma inganta aikin rundunar sojin Nijeriya.”

Ranar Alhamis ne dai Shugaba Tinubu ya ƙara wa Laftanar Janar Shaibu girma bayan majalisar dattawan ƙasar ta tabbatar da naɗin da shugaban ya yi masa na babban hafsan sojin ƙasn Nijeriya. 

Mai magana da yawun sojin ƙasar, Laftanar Kanal Appolonia Aneke, ce ta bayyana sabbin naɗe-naɗen da Janar Shaibu ya yi a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis. 

Ta bayyana cewa Laftanar Janar Shaibu ya yi kira ga manyan hafsoshin da aka bai wa sabbin muƙaman su yi amfani da ƙwarewarsu wajen gina rundunar soji da za ta iya magance matsalolin rashin tsaro da ƙasar ke fuskanta da kuma waɗanda ke kunno kai.

Sanarwar ta ce an mayar da Manjo Janar Bamidele Alabi, ɓangaren tsare-tsare da manufofi a hedkwatar sojin ƙasa a matsayin babban hafsan da ke kula da tsare tsare da manufofi na sojin.

Shi kuma Manjo Janar Jamal Abdulsalam, wanda a baya shi ne babban hafsan da ke kula da ayyuka da shirye-shirye na musamman ya koma ɓangaren gudanarwa a hedkwatar sojin a  matsayin babban hafsan da ke kula da gudanarwa.

Kazalika sanarwar ta ce Manjo Janar Peter Mala ya bar ofishin babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro zuwa hedkwatar horarwa da aƙida ta sojin Nijeriya (TRADOC) a matsayin kwamanda.

Manjo Janar Samson Jiya, daga cibiyar tarihi da makoma ta sojin Nijeriya (NAHFC) zai koma ɓangaren kasafin kuɗi na soji da ke hedkwatar sojin ƙasar.

“Wasu muhimman naɗe-naɗen sun haɗa da Manjo Janar Mayirenso Saraso daga NAHFC zuwa ɓangaren ayyuka na hedkwatar sojin Nijeriya a matsayin babban hafsan da ke kula da ayyukan soji, da Manjo Janar Isa Abdullahi daga hedkwarar tsaro zuwa hedkwatar soji a fannin kula da ma’aikata,” in ji sanarwar.

Kazaliza sauran naɗe-naɗen sun haɗa da na “Manjo Janar Musa Etsu-Ndagi daga ɓangaren horaswa na hedkwatar sojin ƙasa zuwa  ɓangaren hulɗa tsakanin soji da fararen-hula na hedkwatar sojin ƙasar da Manjor Janar Abubakar Haruna daga NAHFC zuwa cibiyar horaswa ta sojin Nijeriya (NATRAC) da ke  Kontagora a matsayin kwamanda.”

Kazalika an sauya wa Manjor Janar Philip Ilodibia wuri daga ɓangaren manufofi da tsare-tsare na hedkwatar sojin ƙasa ta Nijeriya zuwa ɓangaren gudanarwa na sararin samaniya da tsaro a matsayin babban hafsa mai kula da ɓangaren.

Masu AlakaTRT Afrika - Nazarin mulkin Tinubu na shekara biyu: Abin da ya sa ya zama dole a daƙile rashin tsaro a Nijeriya

Shi kuma Manjo Janar Godwin Mutkut, daga rundunar Haɗin Gwiwa na Ƙasashen Yankin Tafkin Chadi (MNJTF) da ke N’Djamena zuwa hedkwatar cibiyar sojojin da ke yaƙi a ƙasa, yayin da aka sauya wa Manjo Janar Umar Abubakar muƙami daga hedkwatar ma’aikatar tsaron Nijeriya zuwa ɓangaren makamai na sojin Nijeriya a matsayin babban kwamanda.

 An sauya wa Manjo Janar John Adeyemo muƙami ne daga makarantar horaswa na yaƙi da manyan makamai na sojin Nijeriya (NASA) zuwa hedkwatar ɓangaren yaƙi da manyan makamai na sojin Nijeriya  a matsayin kwamanda na sojojin da ake amfani da manyan makamai, yayin da Manjo Janar Mohammed Abdullahi daga ya bar cibiyar yaƙi ta intanet zuwa hedkwatar sojin Nijeriya  as matsayin kwamandan da ke kula da sadarwa.

Bugu da ƙari, an sauya wa Manjo Janar Taofik Sidick wuri daga NAHFC zuwa hedikwatar kuɗi na sojin Nijeriya a matsayin babban hafsan harkokin kuɗi da kasafin kuɗi, yayin da aka sauya wa manjo Janar Abdullahi Ibrahim wuri daga NAHFC zuwa  hedkwatar cibiyar manyan bindigogi na sojin ƙasar zuwa a matsayin kwamanda .

Shi kuwa  Manjo Janar Adeyinka Adereti an sauya masa muƙami ne daga hedkwatar tsaro zuwa hedkwatar injiniyoyin lantarki da na injina ta sojin Nijeriya a matsayin kwamanda, yayin da Manjo Janar Nansak Shagaya ya bar ɓangaren ayyukan soji na hedkwatar sojin Nijeriya zuwa zuwa hedkwatar sufuri da samar da kayayyaki na sojin Nijeriya a matsayin kwamanda, sannan aka naɗa Birgediya Janar Yusha’u Ahmed a matsayin muƙaddashin kwamdandan ilimi.

Kazalika babban hafsan sojin ƙasan ya naɗa Manjo Janar Oluyemi Olatoye, daga hedkwatar runduna ta 82 kuma runduna ta musamman ta kudu maso gabashin ta Operation UDO KA zuwa makarantar horas da sojojin Nijeriya (NDA), ta Kaduna a matsayin kwamnda, yayin da Manjo Janar Emmanuel Mustapha daga ma’aikatar da ke kula da shirin sararin samaniya na sojin ƙasa zuwa makarantar sadarwa ta sojin Nijeriya a matsayin kwamanda.

Masu AlakaTRT Afrika - Bayanai kan sabbin hafsoshin tsaron Nijeriya

Manjo Janar Adamu Hassan daga ɓangaren tsaron Nijeriya a Riyadh, zai koma makarantar sojojin da ke amfani da manyan bindigogi a matsayin kwamanda shi kuwa Birgediya Janar John Bulus daga hedkwatar kuɗi ta sojin Nijeriya zuwa makarantar harkokin kuɗi ta sojin Nijeriya a matsayin kwamanda.

Manyan hafsoshi da aka naɗa a matsayin kwamandoji a fagen fama sun haɗa da Manjo Janar Saidu Audu daga ɓangaren horaswa na hedkwatar soji zuwa rundunar haɗin gwiwa ta Yankin Tafkin Chadi (MNJTF) da ke N’Djamena, a matsayin kwamanda da Manjor Janar Warrah Idris daga hedkwatar tsaro zuwa runduna ta musamman ta da ke arewa maso yammacin Nijeriya ta Operation FANSAN YAMMA a matsayin kwamanda  da kuma Manjo Janar Oluremi Fadairo daga ɓangaren hulɗar soji da fararen-hula na hedkwatar sojojin ƙasa zuwa runduna ta 82 ta sojin Nijeriya da ke Enugu a matsayin babban kwamanda da runduna ta musmaman da ke aiki a kudu maso gabashin Nijeriya  ta Operation UDO KA.

Babban hafsan sojin Nijeriya ya kuma naɗa Manjo Janar Olatokumbo Bello a matsayin darakan watsa labaran hedkwatar tsaro ta yayin da aka sauya wa Birgediya Janar Samaila Uba wuri daga makarantsar ƙarin horo wa sojinn Nijeriya na Jaji zuwa hedkwatar tsaro a matsayin daraktan bayanan tsaro.