Bayanai kan sabbin hafsoshin tsaron Nijeriya
NIJERIYA
6 minti karatu
Bayanai kan sabbin hafsoshin tsaron NijeriyaShugaban Nijeriya ya cire Janar Christopher Musa daga matsayin babban hafsan tsaron kasar, inda ya maye gurbinsa da tsohon babban hafsan sojin ƙasa, Janar Olufemi Oluyede.
Sabbin hafsoshin sojin Nijeriya / Others
8 awanni baya

A ranar Jumma’ar da ta gabata ne Shugaba Bola Tinubu na Nijeriya ya sauya manyan hafsoshin tsaron ƙasar.

Shugaban ya cire Janar Christopher Musa daga muƙamin babban hafsan tsaron Nijeriya inda ya maye gurbinsa da Janar Olufemi Oluyede, tsohon babban hafsan sojojin ƙasa na Nijeriya.

Sai Janar Waidi Shaibu wanda ya maye gurbin Janar Oluyede a matsayin babban hafsan sojin ƙasa na Nijeriya.

An bayana sauye-sauyen ne a wata snaarwa da mai magana yawun Shugaban Ƙasar Sunday Dare ya fitar.

Shugaban Ƙasar ya ƙyale Manjo Janar E.A.P. Undiendeye a muƙaminsa na shugaban ɓangaren tattara bayanan sirri na sojin ƙasar.

Sai kuma Shugaba Tinubu ya maye gurbin tsohon babban hafsan sojin ruwa Admiral Emmanuel Ogalla da Real Admiral Idi Abbas.

Shi kuma Air Vice Marshal S.K. Aneke, ya maye gurbin Air Vice Marshal Hassan Abubakar a matsayin babban hafsan sojojin saman Nijeriya.

Ga bayanan da Fadar Shugaban Ƙasa ta gabatar game da sababbin hafsoshin tsaron.

Sabon babban hafsan sojin ƙasan Nijeriya

Manjor Janar Waidi Shaibu wanda ya taɓa kasancewa babban kwamandan Operation Haɗin Kai, an haife shi ne ranar 18 ga watan Disamban 1971 a ƙaramar hukumar Olamaboro ta jihar Kogi.

Ya samu shiga makarantar horas da sojojin Nijeriya da ke Kaduna a shekarar 1989 cikin ‘yan kwas na 41. Ya zama soja mai muƙamin laftanal na biyu ranar 17 ga watan Satumba  na shekarar 1994.

Takardun shaidar karatun da ya samu sun haɗa da shaidar digiri na injiniyan injuna wata mechanical engineering a Turance daga Makarantar horas da sojojin Nijeriya da ke Kaduna.

Sai takardar shaidar kammala karatun bayan digiri na farko wato Post graduate certificate kan gudanarwa daga makarantar koyon gudanar ta Ghana da kuma digiri na biyu kan gudanarwa daga Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Calabar.

Kazalika Manjor Janar Waidi ya samu digiri na biyu kan dabaru na musamman wato Strategic Studies a Jami’ar Ibadan, da kuma digiri na biyu kan dabarun tsaro na musamman wato Strategic Security Studies daga Jamiar National Defence University ta Washington a Amurka.

Har wa yau, Manjo Janar Waidi ya halarci kwas kan shugabanci na ƙarni na 21 a makarantar shugabanci ta Havard Kennedy School of Government da ke Jami’ar Harvard, kuma yana kan karatun digiri na uku kan dabaru na musamman a Jami’ar Ibadan.

Baya ga haka, ya halarci kwasa-kwasai da dama na soji a ciki da wajen Nijeriya.

Sabon babban hafsan sojin ruwa na Nijeriya

Sabon babban hafsan sojin ruwan Nijeriya Rear Admiral Idi Abbas an haife shi ne ranar 20 ga watan Satumban shekarar 1969.

Hafsan, wanda ɗan asalin jihar Kano ne a arewa maso yammacin Nijeriya ya shiga aikin ne ranar 18 ga watan Satumbar shekarar 1992 a kwas na 40 a matsayin mid-shipman.

Ya samu muƙamin Rea'l Admiral ne ranar 10 ga watan Satumban shekarar 2020 bayan ya cika dukkan sharruɗa na aiki da ɗa’a na samun wannan girman.

Rear Admiral Idi Abbas ya riƙe muƙamai daban-daban a tarihin aikinsa a sojin ruwan Nijeriya ciki har da muƙamin kwamandan dakarun sojin ruwa na tsakiya a Bayelsa inda ya taka rawar gani wajen daƙile aika-aikar waɗanda ke satar ɗanyen mai da ‘yan fashin teku a yankin.

A halin yanzu yana aiki ne a cibiyar tarihi da makomar sojin Nijeriya inda yake amfani da ƙwarewarsa wajen tsara manufofi don taimaka wa aikin sojin Nijeriya. Yana da aure da yara.

Babban hafsan sojin sama, Air Vice Marshal Sunday Kelvin Aneke

An haifi Sunday Kelvin Aneke ne ranar 20 ga watan Fabrairun shekarar 1972 a birnin Makurdi na jihar Binuwai, kuma iyayensa ne sojin saman mai ritaya Sylver da Misin Ngozi Aneke.

Ɗan asalin ƙaramar hukumar Udi na jihar Enugu ne a kudu maso gabashin Nijeriya. Air Vice Marshal Aneke ya halarci makarantar yaran sojoji da makarantar horas da sojoji ta NDA da ke Kaduna daga shekarar 1976 zuwa shekarar 1982, inda ya samu shaidar kammala karatun sakandare ta farko.

Ya shiga Marantar Government College ta Kaduna daga shekarar 1982 zuwa shekarar 1987 inda ya samu takardar kammala karatu na Yammacin Afirka wato West African School Certificate.

Air Vice Marshal Aneke ya fara aikin soji ne ranar 10 ga watan Satumban shekarar 1988 a lokacin da ya shiga marantar horas da sojojin Nijeriya NDA a Kaduna  cikin ‘yan kwas na 40.

Daga baya ya fito a matsayin Pilot Officer a rundunar sojin saman Nijeriya ranar 10 ga watan Satumban shekarar 1993.

Yana da digiri a fannin Physics  da kuma diflomar bayan digirin farko kan gudanarwa daga Jami’ar Calabar da kuma digiri na biyu kan diflomasiyya a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Kuma yana karatun digiri na uku kan siyasar tattalin arziƙi da nazarin ci-gaba a Jami’ar Abuja.

Baya ga haka Air Vice Marshal Aneke ya halarci kwasa-kwasai na soji daga ciki da wajen Nijeriya tare da riƙe mahimman muƙamai a sojin ƙasar.

Babban hafsan tattara bayanan sirrin sojin Nijeriya, Manjo Janar Akomaye Parker Nduiandeye

An haife shi ne a Bedia a ƙaramar Hukumar Obudu ta jihar Ribas ranar 2 ga watan Satumban shekarar 1968. Mahaifinsa da mahaifiyarsa su ne Mista Sylvanus da Misis Maria Undiandeye.

Ya halarci makarantar horas da sojojin Nijeriya NDA da ke Kaduna da kuma makarantar horas da sojoji da ke Sandurst a Birtaniya inda ya ƙarasa karatun horas da sojinsa.

Kuma bayan ya zama soja ya halarci kwasa-kwasai da dama ciki har da wanda ya je a makarantar horas da sojoji da ke Jaji.

Babban hafsan ya riƙe muƙamai da dama ciki har da babban hafsa soji a hedikwatar tattara bayanan sirrin sojin Nijeriya, inda ya ja ragamar gudanar da tattarawa da nazari kan bayanan da kuma miƙa su.

Yana da lambobin yabo na aiki daga ciki da wajen Nijeriya.

Hafsan na auren Jane Ekor, kuma suna da ‘ya’ya uku. Ababen da ya fi so sun haɗa da wasan Golf da ɗaukar hoto da kallon hallitu.

Babban hafsan tsaro, Laftanal Olufemi Oluyede

An haife shi ne ranar 21 ga watan Yuni na shekarar 1968 a garin Ikere Ekiti, kuma ɗan asalin ƙaramar hukumar Ikere ne a jihar Ekitio.

Ya halarci makarantar firamare ta Holy Trinity ta Ikere Ekiti, kana ya shiga makarantar sakandare ta Christ’s School da ke Ado Ekiti.

Daga baya ya samu shiga NDA a shekarar 1987 cikin ‘yan kwas na 39. Bayan ya gama karatun horaswar zama laftanal na biyu ranar 19 ga watan Disamban shekarar 1992.

Ya zama babban hafsan sojin ƙasan Nijeriya daga ranar 30 ga watan Oktoba na shekarar 2024 inda ya fara da matsayin muƙaddashi kafin a tabbatar masa da muƙamin.

Hafsan wanda ke da digiri na farko da na biyu kan tattalin arziƙi daga makarantar horas da sojin Nijiriya, ya riƙe muƙamai da dama a sojin Nijeriya.