Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ƙaddamar da dokar da ta kafa cibiyar tsaron intanet ta ƙasar.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito cewar ranar Asabar 11 ga watan Oktoba ne gwamnatin ƙasar ta ƙaddamar da dokar.
Tun shekarar 2022 ne dai Nijar ta zaɓi dabarar tsaron intanet wadda manufarta ita ce tabbatar da cewa ƙasar tana da kafar intanet da ke da cikakken tsaro domin gudanar da harkokin kasuwanci da zamantakewa
Kazalika ta samar da yadda za a aiwatar da dokar ciki har da samar da cibiyar tsaron intanet ta ƙasa, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ambato wata sanarwa daga majalisar ministocin ƙasar tana cewa.
"Manufar cibiyar tsaron intanet ta ƙasar ita ce jagorantar yadda za a ƙaddamar da dabarar tsaron intanet ta ƙasa bisa tsare-tsaren tsaro,” in ji sanarwar.
Kazalika manufar za ta taimaka wajen inganta yanayi na intanet mai inganci ga kasuwanci da zamantakewa a ƙasar, in ji sanarwar.