Turkiyya ta yi maraba da amincewar majalisar dokokin Arewacin Cyprus na Jamhuriyar Turkiyya (TRNC) a ranar Talata kan batun ƙudurin samar da ƙasashe biyu da ya shafi Cyprus.
"Wannan shawarar wata babbar alama ce ta ƙudurin al'ummar Cyprus na Turkiyya na kare 'yancin kai, da asali da kuma makomarsu," kamar yadda mataimakin shugaban ƙasar Turkiyya Cevdet Yilmaz ya wallafa a shafin sada zumunta na NSosyal na Turkiyya.
"Tsarin tarayya, wanda ya kasa taɓuka komai tsawon shekaru da dama, an gaji da shi," in ji shi.

Samun mafita ta haƙiƙa, mai ɗorewa da adalci a tsibirin, zai yiwu ne kawai idan aka samar da ƙasashe biyu masu cikakken iko da daidaito, in ji Yilmaz, yana mai taya 'yan majalisar dokokin TRNC murnar ɗaukar wannan mataki na samar da zaman lafiya da martabar al'ummar yankin Cyprus na Turkiyya.
Turkiyya na bayar da goyon baya ga ‘yan Cyrus na Turkiyya don yanke shawarar kansu da kuma tsara makomarsu zai ci gaba, in ji shi.
Majalisar dokokin TRNC ta amince da ƙudurin da gagarumin rinjaye.
Jamhuriyar Cyprus dai ta kwashe tsawon shekaru dama tana fuskantar rikici tsakanin ‘yan Cyprus na Girka da na Turkiyya, duk kuwa da ƙoƙarin diflomasiyyar shiga tsakani da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi na ganin an cim ma matsaya.
Tun daga shekarun 1960 aka soma hare-haren ƙabilanci wanda ya kai ga tilasta wa 'yan Cyprus ta Turkiyya janyewa zuwa wani wuri don kare lafiyarsu.
A 1974, juyin mulkin da 'yan Cyprus na Girka suka yi da nufin mamaye tsibirin Girka ya janyo tsoma bakin sojin Turkiyya a matsayin masu shiga tsakani don kare ‘yan Cyprus na Turkiyya daga zalunci da tashin hankali. Sakamakon haka ne, aka kafa TRNC a 1983.
An yi ta kwan-gaba-kwan-baya kan batun zaman lafiya a ‘yan shekarun nan, ciki har da wani shiri na 2017 da bai yi nasara ba a Switzerland ƙarƙashin inuwar ƙasashen da suka zama garanto irinsu Turkiyya da Girka da kuma Birtaniya.
Hukumar Kula da Cyprus ta Girka ta shiga Tarayyar Turai a shekarar 2004, sannan a shekarar ne 'yan Cyprus na Girka suka hana wani shirin Majalisar Dinkin Duniya na kawo karshen takaddamar da aka daɗe ana yi.