| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
EFCC ta kama wasu bokaye da dala miliyan 3.4 da €280,000 na jabu a Osun da Lagos
Waɗanda aka kama sun hada da maza biyu da mata uku, kuma an kama su ne a wuraren ibadarsu da ke Jihohin Osun da Legas bayan ayyukan leƙen asiri da EFCC ta jagoranta.
EFCC ta kama wasu bokaye da dala miliyan 3.4 da €280,000 na jabu a Osun da Lagos
EFCC ta kama wasu bokaye da kuɗaɗen jabu dala miliyan 3.4 da €280,000 a Osun da Lagos / EFCC
18 awanni baya

Ma'aikatan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Yankin Ibadan (EFCC) sun kama wasu bokaye biyar a Jihohin Osun da Legas bisa mallakar makudan kuɗaɗen ƙasashen waje na jabu da suka kai dala miliyan 3.43 miliyan da yuro €280,000.

An kama waɗanda ake zargin ne bisa zargin zambatar wata mata mai suna Halima Sanni naira miliyan 26.55, da sunan zummar warware mata matsalolinta da tsarkake ta.

Waɗanda aka kama sun hada da maza biyu da mata uku, kuma an kama su ne a wuraren ibadarsu da ke Jihohin Osun da Legas bayan ayyukan leƙen asiri da EFCC ta jagoranta.

A cewar binciken, wadanda ake zargin suna fakon wadanda ba a san ko su waye ba ta hanyar da'awar cewa suna bayar da magunguna na ruhaniya ga cututtuka daban-daban da kalubalen rayuwa.

An kuma ce sun yaudari wadanda ake zargin da ikirarin suna da rauhanan da za su samar da makuɗan kuɗaɗen kasashen waje, wanda, a cewarsu, yana bukatar tsarkakewar ruhaniya daga wani aljani kafin a kashe kudin.

Masu binciken EFCC sun bayyana cewa ana yaudarar mutanen da cewa sai sun kawo nasu kuɗaɗen, wajen aiwatar da wancan aikin na tsarkakewar.

Baya ga jabun kudaden kasashen waje, jami'an sun kwato motoci biyu na alfarma da wasu wayoyin hannu daga wadanda ake zargin a lokacin aikin.

Hukumar EFCC ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.