Fiye da sojojin Isra’ila 20,000 sun ji rauni tun farkon yakin da aka fara a Gaza a watan Oktoba 2023, inda fiye da rabinsu ke fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa, ciki har da ciwon PTSD (Post-Traumatic Stress Disorder), wato ciwon damuwa bayan fargabar wani lamari mai tsanani, in ji Ma’aikatar Tsaron Isra’ila.
A cewar sashen bayar da shawarwari da farfaɗo da lafiyar ƙwaƙwalwa na ma’aikatar, kusan kashi 56 cikin 100 na waɗanda suka ji rauni sun kamu da ciwon PTSD ko wasu matsalolin lafiyar kwakwalwa, wanda ke nuna irin tasirin matsalar ƙwaƙwalwa da wannan rikici ke haifarwa.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa kusan kashi 45 cikin 100 na waɗanda suka ji rauni suna fama da raunuka a jiki, yayin da kashi 20 cikin 100 na sojojin ke fama da matsalolin kwakwalwa da na jiki a lokaci guda.
An bayyana cewa an yanke wa sojoji 99 gaɓobi inda wasunsu ke da hannaye da ƙafafuwan roba, 16 sun samu shanyewar rabin jiki, 56 na fama da ƙaramar naƙasa sannan wasu 24 sun zama cikakkun naƙasassu
Ma’aikatar ta lura cewa kusan kashi 64 cikin 100 na waɗanda suka ji rauni daga cikin 20,000 din sun kasance sojoji ne na ko-ta-kwana, tare da kusan sabbin sojoji 1,000 da ake kula da su a kowane wata, baya ga ɗaruruwan bukatun da suka shafi yaƙin da ya gabata.
A jimla, sashen bayar da shawarwari da farfaɗo da lafiyar ƙwaƙwalwa yana kula da fiye da tsoffin sojoji 81,000, daga cikinsu 31,000, kusan kashi 40 cikin 100, suna fama da matsalolin ƙwaƙwalwa.
Ma’aikatar ta yi hasashen cewa nan da shekarar 2028, kusan tsoffin sojoji 100,000 za su kasance karkashin kulawarta, inda aƙalla rabinsu ake sa ran za su kamu da PTSD da sauran matsaloli masu alaka.
Sojojin Isra’ila sun kashe kusan Falasdinawa 65,000, mafi yawansu mata da yara, a Gaza tun watan Oktoba 2023. Harin bama-baman da ba ya yankewa ya sa yankin ya zama ba zai iya zama ba, tare da haifar da yunwa da yaduwar cututtuka.