Kamata ya yi 'yan jaridar da ba sa ganin laifin Isra'ila su koma yin labaran bukukuwa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Kamata ya yi 'yan jaridar da ba sa ganin laifin Isra'ila su koma yin labaran bukukuwaMasu sharhi kan yada labarai sun gaya wa TRT World cewa kisan gillar da Isra’ila ke yi wa ‘yan jarida na nufin tilasta daina ba da rahoto daga Gaza, inda suka koka cewa kafofin labarai na Yamma sun gaza goyon bayan 'yan jaridar Falasɗinu.
Isra'ila ta kashe 'yan jarida Falasdinawa fiye da 270 a Gaza a cikin kwanaki 697 da suka gabata, a cewar ƙididdigar Al Jazeera. / AA
3 Satumba 2025

A cikin Gaza da ke ƙarƙashin mamaya, inda ake aiwatar da kisan ƙare dangi, Isra'ila na ci gaba da ɓoye gaskiya tare da kashe masu isar da saƙonni.

A ranar Talata, sojojin Isra'ila sun kashe wasu Falasɗinawa 'yan jarida biyu – Rasmi Jihad Salem da Eman Al-Zamli – wadanda suka shiga jerin sunayen 'yan jarida da aka kashe a rikicin da ake ganin shi ne mafi haɗari ga ma'aikatan kafofin watsa labarai a duniya.

Jami'an Falasdinu sun bayyana cewa Salem, wanda ke aiki da Kamfanin Manara Media, an kashe shi a wani hari da Isra'ila ta kai a titin Abu al-Amin kusa da dandalin al-Jalaa a birnin Gaza.

Haka zalika, a arewacin birnin Khan Younis, Isra'ila ta yi amfani da jirgin sama mara matuki wajen kashe 'yar jarida Al-Zamli yayin da take neman ruwan sha a kusa da unguwar Hamad City.

A cewar ƙididdigar Al Jazeera, Isra'ila ta kashe 'yan jarida Falasdinawa 274 a Gaza tun daga watan Oktoban 2023 – ban da Salem da Al-Zamli – wadanda aka wallafa sunayensu a wani sabon bidiyo da aka yaɗa.

Isra'ila ta hana kafofin watsa labarai na ƙasa da ƙasa damar ba da rahoto kan abin da ke faruwa a Gaza yayin da take jagorantar 'yan jarida daga ƙasashen da take ƙawance da su wajen ɗaukar labaran da suke so.

Kafofin watsa labarai suna dogara ne da 'yan jarida Falasdinawa da mazauna Gaza don bayyana wa duniya abin da ke faruwa.

Duk da haka, Isra'ila tana yawan tambayar dangantakar 'yan jarida Falasdinawa da ke bayar da rahoto kan wannan rikici, amma ba ta ba da izinin shigar 'yan jarida daga ƙasashen waje ba.

Masu nazari kan harkokin kafofin watsa labarai sun nuna cewa yayin da Isra'ila ke kokarin hana yin rahotanni daga Gaza, kokarinta bai samu kalubale daga wasu kafofin watsa labarai na Yammacin Duniya ba, wadanda suka kasa tallafa wa abokan aikinsu na Falasdinu.

Ian Williams, Shugaban Kungiyar 'Yan Jarida ta Kasashen Waje (FPA), ya shaida wa TRT World cewa, "Isra'ila tana so ta rufe bakin kafofin watsa labarai baki ɗaya sai dai ba za ta iya hana mummunar tsanar da take fuskanta daga kowane sashe na duniya ba. Duk rashin mutuncin da Isra'ila take yi yana ƙara rusa martabarta a idanun duniya."

Williams ya soki kafofin watsa labarai na ƙasashen waje, musamman daga Ƙasashen Yamma, saboda rashin daukar halin da 'yan jarida Falasdinawa ke ciki da muhimmanci, yana mai cewa bai kamata a amince da su kan ba da rahoton "batutuwa masu muhimmanci ba."

Ya kara da cewa, "Ba za a iya yi musu uzuri ba. Duk wani dan jarida da bai nuna ɓacin rai kan wannan mummunan abu ba, ya kamata kawai su koma ba da rahoto kan bikukuwan aure da tarukan kwalliya da kayan ƙawa, su daina rahoto kan batutuwan duniya masu muhimmanci."

Ya kuma bayyana cewa, "Halayen 'yan jarida suna da alaka kai-tsaye da halin da mutanen Gaza ke ciki."