A yayin da Torben, wani likita kuma masanin kimiyya daga Jamus, ya yanke shawarar bin ayarin jiragen ruwan Sumud na kasa da kasa da ke dauke da tallafi zuwa Gaza da Isra’ila ta mamaye, ya san yana da abubuwa da dama da zai yi asara.
Amma, ya ce ba komai ba ne idan aka kwatanta da irin wahalhalun da miliyoyin mutane da ke fama da yunwa da da rabuwa da matsugunansu ba a Gaza.
"Ina jin tsoro, kuma tabbas, ina da damuwa, amma ni mutum ne mai basira da ya yanke shawarar yin abin da ya dace," Torben, wanda ya bayyana sunansa na farko saboda dalilai na tsaro, ya shaida wa TRT World a Tunisia.
"Wannan ne dalilin da ya sa na shiga cikin wannan yunƙuri na kawo agaji zuwa Gaza," in ji shi.
Ayarin jiragen ruwan Sumud shi ne na baya bayan nan kuma mafi girma ya zuwa yau don fara aikin kawo karshen mummunan shingen da Isra'ila ke yi, wanda ya sanya yunwa ta yi ajalinmutane 185 a Gaza cikin wata guda.
Adadin wadanda suka mutu sakamakon yunwa tun daga watan Oktoban 2023 ya kai 348. Hukumar kula da yunwa ta duniya da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, ta tabbatar da hakan a hukumance.
Tsoron kame ko lmari mafi muni
Kimanin masu fafutuka 300, 'yan siyasa da masu fasaha daga kasashe 44 dauke da kayan agaji zuwa Gaza sun tashi daga tashar jiragen ruwa ta Barcelona da yammacin ranar Litinin.
Wasu manyan kawance guda hudu ne suka shirya wannan tafiya, da nufin karya shingen ƙawanya da Isra'ila ta yi a Gaza da kuma bai wa Falasdinawa taimakon da suke bukata.
Torben ya ce "Na dade ina jin rashin karfi a kasar da jama'a da kafafen yada labarai ke da hannu a kisan kiyashin da ke faruwa."
Yayin da ayarin jiragen ruwan ya fara tafiya a ranar Litinin, yanayin ya kasance cikin kwanciyar hankali da jimami.
Mutane da yawa sun damu, sanin cewa suna adawa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, wanda yake ta aikata ta’annati ba tare da fuskantar wani hukunci ba tun lokacin da Isra'ila ta kaddamar da yakinta a Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Tsoron kamawa ko fuskantar abu mafi muni na kai komo saboda babu adalci kasafai, ko da bayan Isra'ila ta kashe mutane sama da 63,000, da suka hada da da 'yan jarida 247 da yara da jarirai, tun daga ranar 7 ga Oktoban 2023.
"Na damu, e, amma kasancewa a nan tare da duk sauran mahalarta da ke da ƙarfin hali na taimaka mini wajen shawo kan wannan damuwa," in ji shi.
A yayin da ayarin farko, wanda ya kunshi dimbin kananan jiragen ruwa na farar hula, wadanda suka tashi daga tashar jiragen ruwan Spaniya, mahalarta taron sun yi shewa suna fadin ‘Yancin Falasdinu’ tare da daga tutar kasar.
Rukunin jiragen ruwa na biyu na shirin tashi daga Tunisiya a ranar 4 ga Satumba, wanda za su hade da jiragen ruwan da suka taso daga Italiya, Girka, da sauran wuraren da ke gaba da Bahar Rum.
"Wannan ita ce manufa mafi girma ta hadin kai a tarihi, inda aka tattara mutane da jiragen ruwa fiye da duk yunkurin da aka yi a baya," in ji mai fafutuka dan kasar Brazil Thiago Avila a wani taron manema labarai a Barcelona.
Kasashe daga nahiyoyi shida ne ke shiga cikin wannan yunkuri da suka hada da kasashen Australia da Afirka ta Kudu da Brazil da kuma kasashe da dama daga kasashen Turai da ke kokarin lalata haramtacciyar mamayar Isra'ila a Gaza.
Ayarin za su dauki kwanaki bakwai zuwa takwas don yin tafiyar kusan kilomita 3,000 zuwa Gaza.
Falasdinawa na fuskantar hatsari mafi girma
A Tunisiya, Moa Jihad, wani Bafalasdine dan Ramallah, duk da cewa bai iya shiga cikin ayarin ba, ya kwashe sa'o'i yana jiran isowar ayarin farko na jiragen ruwan.
"Ayarin jiragen ruwan Sumud zai sake zuwa Gaza yana mai tunatar da mutane cewa ana kashe Falasdinawa da hana su abinci, kuma ana ci gaba da yin kisan kare dangi; jama'a na shan wahala," kamar yadda ya shaida wa TRT World.
"A yau mun tsaya a nan don tallafa wa aikin ko da ba zan iya shiga ba."
Moa na fuskantar hatsarin kamawa ko cutarwa fiye da mutanen wasu kasashe saboda yana da fasfo din Falasdinu.
Moa ya ce "Idan sojojin Isra'ila suka kama ni suka sa ni a gidan yari, to kenan zan kasance a gidan yari tsawon shekaru 10 ko ma fiye da haka."
"Don haka na zo nan don nuna godiyata ga duk wanda ke da niyyar karya ƙawanyar."
Tun daga shekarar 2007, Isra'ila ta kwace iko da sararin samaniyar Gaza da tekun yankin, tare da takaita zirga-zirgar kayayyaki da mutane sosai. Babu filin jirgin sama mai aiki bayan da Isra'ila ta kai harin bam tare da lalata filin jirgin sama na Gaza a shekara ta 2001.
Don haka, lokacin da aka toshe hanyoyin samar da kayayyaki da aka saba amfani da su, kamar sararin samaniya da hanyoyin mota, sai ake shirya wani aiki kamar Jirgin Sumud. Sumud kalma ce ta Larabci da ke nufin "juriya".
Masu fafutuka da ke goyon bayan Falasdinu, da suka hada da mai fafutukar sauyin yanayi Greta Thunberg da dan wasan kwaikwayo Liam Cunningham na cikin ayarin.
Furodusan TRT Français, Sena Polat, ita ma na ɗaya daga cikin mahalarta taron da ke jira a Tunisiya don shiga jirgin ruwan Sumud tare da tafiya zuwa Gaza.
Gwagwarmayar da aka kafa a shekarar 2006 a lokacin da ake tsaka da yakin da Isra'ila ke yi a Lebanon, gwagwarmayar ta kaddamar da jiragen ruwa 31 tsakanin shekarar 2008 da 2016, inda biyar suka samu nasarar isa Gaza duk da tsauraran matakan da Isra'ila ke dauka.
Duk da haka, tun daga shekara ta 2010, duk wani jirgin ruwa da ke ƙoƙarin karya shingen da aka yi wa Gaza, Isra'ila na kama shi ko kuma fuskantar kalubalanta a iyakar tekun Isra;’ila.
Harin da aka kai kan jirgin ruwan Mavi Marmara a shekarar 2010 ya yi sanadiyyar mutuwar masu fafutuka 10 tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ya janyo cece-kuce a duniya.
Torben ya kara da cewa "Ni ba dan gwagwarmaya ba ne ko jarumi ko wani abu banda mutum mai hankali da ya yanke shawarar yin abin da ya dace."
"Ina da dangi, ina da abokai, ina da buri a Jamus, kuma ina da abubuwa da yawa da zan yi asara, amma kun san ba kome ba ne idan aka kwatanta da wahalar da ake sha a Gaza."
Furodusan TRT Français Sena Polat ta bayar da gudunmawa wajen rubuta wannan rahoto daga Tunisia.