GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Shugabannin Musulmi sun yi kira a ɗauki mataki kan harin 'wulaƙancin' Isra’ila da ajandar mamaya
Manyan yara na Falasṭin suna mutuwa kafin su kai shekara ɗaya a ƙarƙashin ƙarƙashin Isra'ila.
Shugabannin Musulmi sun yi kira a ɗauki mataki kan harin 'wulaƙancin' Isra’ila da ajandar mamaya
Mahalarta taron gaggawa na Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi sun ɗauki hoto bayan taron a Qatar. / Reuters
15 Satumba 2025

Al'ummar Musulmi sun ci gaba da yin tofin Allah tsine a ranar Litinin a daidai lokacin da kasar Qatar ke gudanar da wani taron gaggawa na Ƙasashen Larabawa da na Musulmi a birnin Doha, inda shugabannin kasashen suka yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai kan masu sasantawa na Hamas a birnin Doha.

Qatar

Da yake jawabi a wajen taron, Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya ce harin da Isra'ila ta kai na matsorata ne da ha'inci, yana mai cewa shugabannin Hamas suna nazari ne kan kudirin tsagaita wuta da Amurka da Qatar da Masar suka gabatar musu a lokacin da aka kai harin.

Turkiyya

Taron Ƙasashen Larabawa da Musulunci da ake yi yanzu haka a Doha babban birnin kasar Qatar, wanda aka gudanar bayan harin da Isra'ila ta kai a birnin a makon da ya gabata, na nuni da irin goyon bayan da Ƙasashen Musulmin duniya suke bai wa kasashen yankin Gulf, in ji Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan a jawabin da ya yi a taron Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmi ta OIC da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa.

Ya kara da cewa, "Muna fuskantar tunanin 'yan ta'adda na Isra'ila da ke ci gaba da jawo hargitsi da zubar jini, da kuma kasar da ke goyon bayanta," yanai mai da cewa, "Dole ne mu ƙara ƙaimi a fannin diflomasiyya" don ƙara azama kan kasar Isra'ila.

Masar

Shugaban Masar Abdel Fattah el Sisi ya yi gargadin cewa abin da Isra'ila ke yi na yin illa ga yarjejeniyar zaman lafiya a halin yanzu.

"Abin da ke faruwa a yanzu yana lalata makomar zaman lafiya, yana barazana ga tsaronku da kuma tsaron dukkan al'ummomin yankin, kuma yana kawo cikas ga duk wani fatan sabbin yarjejeniyar zaman lafiya," in ji Sisi.

"Haka kuma yana lalata yarjejeniyoyin zaman lafiya da ake da su da kasashen yankin, sakamakon zai yi muni, inda yankin zai koma wani yanayi na tashe-tashen hankula da kuma asarar kokarin samar da zaman lafiya mai dimbin tarihi da nasarorin da aka samu ta hanyarsu. Wannan wani abu da zai shafi kowa a cikinmu ba tare da ware wani ba.”

Jordan

A nasa bangaren, Sarkin Jordan Abdullah II, ya yi kira da a mayar da martani mai karfi a yankin.

"Martaninmu game da cin zarafi da aka yi Qatar dole ne ya kasance a fili mai ma’ana kuma wanda zai zama gargaɗi, saboda barazanar Isra'ila ba ta da iyaka," in ji shi a taron.

Iran

Harin da Isra'ila ta kai kan Qatar "aikin ta'addanci ne ƙarara, wanda ya ƙetare duk wani jan layi," in ji shugaban na Iran yayin jawabinsa a wajen taron, yana mai jaddada cewa ana bukatar hadin kan Musulunci don mayar da martani.

Ana zargin Isra'ila da aikata kisan kare dangi a kan Falasdinawa a Gaza, ciki har da kisan ƙare dangi kan kungiyar manyan malaman duniya, a yakin da ta yi na kusan shekaru biyu a yankin Falasdinu da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 64,000.

Qatar ta kasance babbar mai shiga tsakani a yakin Isra'ila a Gaza kuma ta zargi Isra'ila da yin zagon kasa ga samun zaman lafiya da Netanyahu da aikata "ta'addancin kasa".