Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, wanda ya karɓi baƙuncin shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz a Ankara, ya jaddada cewa Turkiyya da Jamus za su iya taka muhimmiyar rawa wajen yin aiki tare domin kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila a Gaza.
Da yake gabatar da jawabi tare da Merz bayan ganawarsu a ranar Alhamis, Erdogan ya soki hare-haren da Isra'ila ta kai a Gaza a baya bayan nan kuma ya buƙaci Jamus ta ɗauki mataki mai tsauri kan hakan.
“Hamas ba ta da bama-bamai ko makaman nukiliya, amma Isra’ila na da su, kuma ta yi amfani da su wajen kai hari Gaza jiya,” in ji Erdogan. Yana mai ƙari da cewa “shin Jamus ba ta ga hakan ba ne?”
Erdogan ya ce Turkiyya da Jamus, a matsayinsu na ƙasashe waɗanda ke da tasiri kana suke taka muhimmiyar rawa a yankin da duniya baki ɗaya, za su iya yin aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya a Gaza.
"Turkiyya da Jamus ƙasashe ne masu mahimmanci da za su iya yin aiki tare domin kawo ƙarshen yaƙin Gaza," in ji shi.
Erdogan ya yi kira ga ƙungiyoyin agaji, ciki har da Red Cross ta Jamus da Red Crescent ta Turkiyya, da su ɗauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen kisan ƙare-dangi da yunwa a Gaza.
"Dole ne Red Cross ta Jamus da Red Crescent ta Turkiyya su ɗauki mataki domin dakatar da kisan ƙare-dangi da yunwa a Gaza," in ji shi.
Kalaman na Erdogan sun zo ne bayan da Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 100, ciki har da yara 46, a Gaza a ranar Talata da yamma, matakin da ya keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma tun ranar 10 ga watan Oktoba.
















