Kamfanin makamashin nukiliya na ƙasar Faransa Orano ya ce yana da tan 1,500 na sinadarin uranium a kamfanin ma’adinai na ciki gida SOMAIR da ke arewacin Nijar, kana ya buƙaci a biya shi diyya idan har an kama ko kuma sayar da kayan ne ba tare da izininsa ba.
Orano ya nemi a cibiyar sulhu ta ƙasa da ƙasa ta bankin duniya ta shiga tsakaninsa da Nijar a watan Janairu bayan da gwamantin sojin ƙasar ta hana kamfanin ayyukansa a SOMAIR kafin ta mayar da shi na ƙasa.
Nijar ta kasance ƙasa ta bakwai a duniya da ke samar da sanadarin uranium da na maganin cutar kansa, kazalika ita ke samarwa kamfanin Orano kashi 15 cikin 100 na sinadarin uranium a lokackin da kamfanin ke aikin haƙo ma’adinai sosai a ƙasar.
Kwace kaso 63.4 na hannun jarin Orano da Nijar ta yi, ya bayyana irin gagarumin sauyin da aka samu a yankin, inda gwamnatocin da sojoji ke jagoranta a ƙasashen Mali da Burkina Faso da Guinea ke ƙoƙarin ƙarfafa ikonsu kan albarkatun ƙasa da suke da su.
Ribar farashi
A ranar 23 ga watan Satumba ne wata kotun bankin duniya ta umarci Nijar ta dakatar da yarjejeniyar sayarwa ko kuma aika da sinadarin uranium da kamfanin Orano ya ce an haƙo shi kafin gwamnatin sojin ƙasar ta dakatar da ayyukan kamfanin.
‘‘Kamfanin ba shi da wani bayani game da ci gaba da samar da sinadarin daga wurin haƙo shi,’’ a cewar wata amsar tambaya ta imel da Orano ya aika wa kamfanin dillacin labarai na Reuters.
"A iyakar saninmu, har yanzu uranium da muka tara yana adane a SOMAIR," in ji saƙon. Yayin da farashin tan ɗin uranium ya kai $82, jimullar sinadarin da Orano ya tara a ma'ajiyar SOMAIR ya kai kusan dala miliyan 270.
Farashin ya ƙaru da kusan kashi 30 tun a tsakiyar watan Maris sai dai yanzu yana ƙasa da $106 da aka taɓa kaiwa a Fabrairun 2024.
Haƙo ma’adinai a ƙarƙashin sa idon gwamnati
Orano ya ƙi cewa komai game da masu son sayen sinadarin da ke zuwa Nijar, yana mai mayar da hankali wajen sulhu.
A nata ɓangaren, gwamnatin Nijar ba ta mayar da martani ba a yayin da aka buƙaci jin ta bakinta ba.
Majiyar SOMAIR ta shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa kimanin tan 1,570 na uranium aka ajiye a wurin adana ma'adinan.
‘‘A yanzu hukumar SOPAMIN (Société du patrimoine des mines du Niger) ta Nijar ce take sa ido kan ma’adinan ƙasar’’ in ji majiyar.
Ya samar da dubban tan na uranium
‘‘A iya sanina, babu wata cinikayyya a hukumance da aka gudanar,’’ in ji majiyar, inda ta nemi a sakaya sunanta saboda gimar batun. ‘‘Akwai buƙata sosai da ake ta samu.’’
Kamfanin SOMAIR ya samar da tan 70,000 na uranium kusa da birnin Arlit tun daga shekarun 1970.
Gwamnatin sojin Nijar, wadda ta yi juyin mulki a watan Yulin shekarar 2023, ta ƙara ƙarfafa ikon mallakar zinari da man fetur da kuma kwal na Nijar.
A yayin babban taron Majalisar Dinkin Duniya, Firaministan ƙasar Ali Lamine Zeine, ya zargi kamfanonin ƙasashen waje da kwashe shekaru suna satar ma’adinan Nijar, yana mai cewa sinadarin uranium ya janyo wa ‘yan Nijar wahalhalu, da gurɓacewar yanayi da tawaye da cin hanci da rashawa da kuma halin ƙaƙa-ni-ka-yi” yayin da ɗaya ɓangaren kuma ya wadatar da Faransa.