TURKIYYA
2 minti karatu
Za a gudanar da tattaunawa a Istanbul kan yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza da matsalolin jinƙai
Ana sa ran taron zai haɗa ministocin harkokin wajen ƙasashen Turkiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Indonesiya, Qatar, Pakistan, Saudiyya, da Jordan – waɗanda suka gana da Shugaban Donald Trump a Satumba, a gefen babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya.
Za a gudanar da tattaunawa a Istanbul kan yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza da matsalolin jinƙai
Ana sa ran Fidan zai yi Allah wadai da ƙoƙarin Isra'ila na neman dalilai don kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita wuta / AP
2 Nuwamba 2025

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, zai karbi baƙuncin wani taro kan Gaza a birnin Istanbul a ranar Litinin, kamar yadda majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya suka bayyana.

Ana sa ran taron zai haɗa ministocin harkokin wajen ƙasashen Turkiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Indonesiya, Qatar, Pakistan, Saudiyya, da Jordan – waɗanda suka gana da Shugaban Amurka Donald Trump a ranar 23 ga Satumba, a gefen babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya, kamar yadda majiyoyin suka bayyana a ranar Lahadi.

Za a tattauna kan sabbin abubuwan da suka faru dangane da yarjejeniyar tsagaita wuta ta ranar 10 ga Oktoba da kuma halin jinƙai a Gaza.

Ana sa ran Fidan zai yi Allah wadai da ƙoƙarin Isra'ila na neman dalilai don kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita wuta, yana mai jaddada cewa dole ne al'ummar duniya su ɗauki matsaya mai ƙarfi kan matakan tayar da hankali na Tel Aviv.

Haka kuma, zai jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin ƙasashen Musulmi don tabbatar da cewa yarjejeniyar tsagaita wuta ta zama zaman lafiya mai ɗorewa.

Taimakon jin kai da bai isa ba

Ana sa ran Fidan zai jaddada cewa taimakon jin ƙai da ake shigarwa Gaza a yanzu bai isa ba, kuma Isra'ila ta gaza cika wajibcinta a wannan muhimmin batu.

Yana mai jaddada cewa tabbatar da isar da taimakon jinƙai mai yawa ba tare da katsewa ba ga Gaza wani abu ne na jinaiƙ da kuma wajibi na doka, zai kuma bayyana cewa ya zama dole a matsa lamba kan Isra'ila don ta cika waɗannan buƙatun.

Ana sa ran Fidan zai yi kira da a gaggauta aiwatar da shirye-shiryen da za su ba Falasɗinawa damar ɗaukar nauyin tsaro da gudanar da Gaza, tare da kare haƙƙinsu na halal da kuma tabbatar da hangen nesa na mafita ta ƙasashe biyu.

Haka kuma, zai jaddada muhimmancin ci gaba da yin shawarwari da haɗin kai kan matakan da za a ɗauka a cikin dandamalin Majalisar Ɗinkin Duniya, kamar yadda majiyoyin suka ƙara da bayani.