AFIRKA
1 minti karatu
Burkina Faso ta yi shelar bai wa duk ‘yan Afirka damar samun bizar shiga ƙasarta kyauta
Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar Pingdwendé Gilbert Ouédraogo ya ce matakin wani ɓangare ne na manufar son kishin Afirka na Shugaba Ibrahim Traoré.
Burkina Faso ta yi shelar bai wa duk ‘yan Afirka damar samun bizar shiga ƙasarta kyauta
Majalisar ta ɗauki matakin ne a a wani ɓangare na manufar kishin Afirka na Kyaftin Traoré / Reuters
12 Satumba 2025

Burkina Faso ta yi shelar bai wa duk ‘yan Afirka izinin shiga ƙasarta kyauta a matsayin wani ɓangare na matakan da majalisar ministocin ƙasar ta ɗauka a zamanta na mako-mako da shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya Kyaftin Ibrahim Traoré ya jagoranta.

Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar, Pingdwendé Gilbert Ouédraogo a ranar Alhamis ya ce majalisar ta ɗauki wannan matakin ne a matsayin wani ɓangare na manufar kishin Afirka na Kyaftin Traoré.

“Daga yanzu, ko wane ɗan nahiyar Afirka da ke son zuwa Burkina Faso ba zai biya kuɗi wajen neman izinin shiga ƙasar ba,” in ji Ministan Tsaro Mahamadou Sana.

Sana ya bayyana cewa manufar dokar ita ce “ƙarfafa tafiye-tafiyen ‘yan Afirka ba tare da da kayayyakinsu a cikin ƙasar Burkina Faso da kuma haɗewar Afirka.”

Sai dai kuma, ya yi ƙarin haske cewa sabon shirin “ba ya nufin  ɗauke wa mutane neman biza.”