Fasinjoji 19 sun rasa rayukansu a ranar Asabar a lokacin da wata motar haya ɗauke da amarya da wasu ‘yan biki ta faɗa cikin kogi.
Motar ta faɗa cikin a kogin ne a lokacin da take yunƙurin tsallake wata gada da ta karye wadda ke tsakanin ƙauyen Gwalli da garin Gummi a Jihar Zamfara.
Mutanen da abin ya rutsa da su taso ne daga Ƙauyen Fass a Ƙaramar Hukumar Gummi zuwa Jihar Kebbi domin kai amarya wurin mijinta bayan an kammala aure.
Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa direban motar, wanda bai saba da hanyar ba, ya yi ƙoƙarin ƙetare gadar wadda jama’ar ƙauyen suka yi wa cuko da yashi da duwatsu.
A cewar Muhammad Fatihu, motar ta zame daga inda aka cike da duwatsu ta kuma kife a cikin kogi, lamarin da ya jawo nutsewar fasinjojin.
Wani ɗan uwa ga waɗanda abin ya shafa, Ummaru Tela Gwalli, ya bayyana cewa motar ta yi lodi fiye da kima, kuma direban ya firgita a lokacin da ya ji motar tana gogar duwatsun da aka yi amfani da su wajen rufe ramin gadar.
“Direban ya tsaya ya duba, sai amarya tare da wasu daga cikin mutanen motar suka sauka daga motar cikin sauri. Abin takaici, lokacin da direban yake waje, motar ta karkata ta gefen dama na gadar inda ta faɗa cikin kogi,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa mutane 19 ne suka mutu a wannan haɗari. An samo gawawwaki 17, yayin da guda biyu har yanzu ba a gano su ba.
Amarya da ƙalilan daga cikin fasinjojin da suka sauka daga motar ne suka tsira, amma duk sauran waɗanda suka rage cikin motar sun nutse.
Da yake tabbatar da wannan mummunan lamari, Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara kuma dan majalisa mai wakiltar Gummi II, Hon. Adamu Aliyu Gummi, ya bayyana lamarin a matsayin abin tausayi.
Ya koka da cewa duk da yawan roƙo da aka yi, gadar ta ci gaba da kasancewa cikin lalacewa fiye da shekara biyar.