Daga Endashaw Aderie
Yayin da shugabannin duniya ke shirye-shiryen taron koli na yanayi na Afirka da kuma sanya tunaninsu kan taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya (COP30) mai zuwa a watan Nuwamba, tattaunawar da jama'a za su yi za ta fi mayar da hankali kan manyan yarjeniyoyi da kuma bayyana aniyar kawo sauyi.
Amma ga al'ummominmu na Gabashin Afirka, matsalar yanayi ba barazana ce mai nisa ba. Wannan lamari ne na gaggawa ga lafiya a yau, wanda ke kara bayyana a yawan cututtukan da aka manta da su a fadin yankinmu.
A kowace rana, a wasu yankunan Afirka da ke fama da matsanancin munin sauyin yanayi da rikice-rikice, muna shaida lamri mai muni amma ba a bayyana shi: sauyin yanayi ba wai yana kara ta'azzara afkuwar ibtila’o’i ba ne, har ma yana hanzarta yaduwar cututtuka masu saurin kisa, da aka yi sakaci a kan su a kasashe masu zafi.
Waɗannan cututtuka sun daɗe suna addabar al'ummomin duniya masu rauni, amma a yau, yanayin zafi, rashin ruwan sama, da matsanancin yanayi na sake fasalin yanayin su kuma suna ƙara yin tasiri.
Wadannan batutuwa masu karuwa da suka shafi yanayi da kiwon lafiya sun zo a daidai lokacin da ake samun gagarumin raguwar agajin jinƙai da ci gaba, wanda zai kara dagula al'amuran kiwon lafiya a yankin.
Kungiyoyi Likitocin Komai da Ruwanka ta Médecins Sans Frontières ko Doctors Without Borders (MSF) da ke yankunan na ganin yadda al’amuran ke wakana a zahiri. Illar sauyin yanayi da rashin kyakkyawan tsarin kula da lafiya, da sakaci na haduwa wajen janyo asarar rayuka.
A wuraren da ake fama da busassun yanayi na arewacin Kenya, fari da ya dauki tsawon lokaci da ruwan sama da ba a iya hasashen sa ba, ya tilasta wa al'ummomi makiyaya yin tafiye-tafiye zuwa inda za su samu ruwa da wuraren kiwo, wanda hakan ke kara kusantar da su ga cututtuka irin su kudan yashi, wadanda ke yada cutar kala azar.
A kasar Sudan ta Kudu da ke fama da ambaliyar ruwa, wata ambaliyar ruwa mai tsanani ta janyo yawaitar dodon kodi da dama a tsakanin jama’a wanda ke sanya cutar tsargiya.
Yawaitar bullar cututtukan
A ƙarshen 2024, an sami gagarumin ƙaruwar kamu wa da cutar kala azar (visceral leishmaniasis) inda ta mamaye yankunan Marsabit da Wajir a Kenya.
Ya zuwa tsakiyar watan Mayun 2025, an samu bullar cutar kala azar har sau 347, da kuma asarar rayuka biyar a Marsabit, yayin da Wajir ya samu masu dauke da cutar su 994 da kuma samun mutuwar mutane 40, inda yara ‘yan kasa da shekaru biyar ne suka fi yawa.
Kala azar cuta ce mai saurin kisa da ƙudaje ke yada wa a cikin yanayin zafi busasshe, yanayin da sauyin yanayi ke ta’azzara wa.
Tana haifar da zazzaɓi na tsawon lokaci, da janyo rama mai tsanani da kuma ƙara girman uwar hanji, kuma tana janyo asarar rayuka a sama da kashi 95 na wadanda suka kamu da cutar idan har ba a ba su kulawar da ta kamata ba; Kala azar ita ce ta biyu bayan zazzabin cizon sauro a tsakanin cututtukan da kwayoyin cuta na parasite ke janyo wa.
Cutar na da wahalar gano wa, al'ummomi da yawa ba su fahimce ta ba, kuma galibi tana fuskantar jinkirin jinya saboda ƙarancin kayan gwaji da magunguna a duniya.
Ko da a inda Kungiyar Komai da Ruwanka za ta iya ba da magani ga marasa lafiya da horar da ma'aikatan kiwon lafiya, batutuwa masu mahimmanci kamar sauyin yanayi, rashin kyakkyawan tsarin kula da lafiya na ci gaba da haifar da yaduwar cutar.
Tsargiya
A kan iyaka, a garin Old Fangak mai nisa da ke jihar Jonglei, Sudan ta Kudu, wata cuta da ba a kula da ita ta yadu: Tsargiya.
Garin Old Fangak na da saurin samun ambaliyar ruwa, wanda hakan ke haifar da yanayin yaduwar cututtuka, wadanda ƙwayoyin cuta da ake samu a cikin dodon kodi na cikin tafkuna da koguna ke haifarwa.
Binciken MSF na 2022 ya nuna cewa aƙalla kashi 84% na ‘ƴan makaranta a Old Fangak suna ɗauke da ƙwayar cutar ta tsargiya.
Duk da yaɗuwar cutar, an sami ƙarancin gangamin samar da magunguna a yankin, musamman saboda yadda ba a samun magungunan.
Ƙungiyoyin MSF suna zargin cewa yawancin mata da 'yan mata a Old Fangak na iya fama da cutar tsargiya mai karfi, musamman ma tsargiyar farjin mata, wadda ke da tsanani kuma ake yin biris da ita.
Jami’an MSF sun ba da kulawa a asibitin Old Fangak har zuwa lokacin da jiragen sama masu saukar ungulu guda biyu suka jefa bama-bamai a a yankin a watan Mayun nan, inda suka lalata dakin magani da muhimman kayan kiwon lafiya, wanda hakan ya sa ba da kulawar jinya a wurin ba zai yiwu ba.
Halin da ake ciki a Jonglei karamin misalin abinda ke faruwa a Gabashin Afirka ne. Sauyin yanayi yana haifar da yanayi mai kyau ga cututtuka da aka yi watsi da su don su bunƙasa; duk da haka, rikice-rikice da rashin kulawa a duniya sun hana a dauki matakin da ya dace.
Mutanen da suka fi fama da rauni, makiyaya, mata, da yara suna ci gaba da fuskantar illolin wannan biris din da aka yi.
Tasirin Watsi da lamarin
Abubuwan da ke da alaƙa da yanayi, ko ambaliya, fari, ko zafi, ba kasafai suke zama rikici ɗaya ba.
Suna haifar da illa mai yawa: mutuwar amfanin gona, ƙarancin ruwa, rashin abinci mai gina jiki, kuma a ƙarshe, bullar cututtukan da ke cinye jiki mai rauni.
A ayyukanmu, muna ganin cutar kala azar da tsargiya suna fitowa tare da kwalara, zazzabin cizon sauro, da rashin abinci mai gina jiki.
Muna tura jami’an kula da lafiya na tafi-da-gidanka don isa ƙauyuka da suke a keɓe, muna saka ruwa, tsaftar muhalli, da matakan tsafta a cikin matakanmu na likitanci, da horar da ma'aikatan kiwon lafiya na gida don gano wa da magance waɗannan cututtuka da wuri.
Amma waɗannan ayyukan ceton rai ba su isa ba sai an samar da tsari sosai.
Cututtukan da ake samu a yankuna masu zafi na da hatsari game da yanayi kuma ba a kashe kudaden da suka kamata don magance su.
Cire su daga dabarun yaki da sauyin yanayi ya sanya an tsallake matakin kare al’ummu masu rauni, wanda har ana samun asarar rayuka, jin dadin rayuwa, neman ilimi da karuwar talauci.
Yin watsi da waɗannan cututtuka kuma yana yin barazana ga kula da lafiyar duniya yayin da sauyin yanayi ke fadada zuwa wuraren zama da kuma yada cututtukan zuwa sababbin wurare. Ba za mu iya samun damar jiran wannan faɗaɗa ta girmama ba kafin mu yi aiki.
Cikin gaggawa ana bukatar haɗin kai, da tsarin kiwon lafiya mai jure sauyin yanayi.
A MSF, muna aiki da la’akari da hatsarin sauyin yanayi a cikin shirinmu na ayyuka. Wannan yana nufin samar da kayan aikin likitanci kafin ambaliya ta raba al'ummomi, bin diddigin alamun muhalli wanda zai iya nuna yiwuwar barkewar wata matsala, da kokari gano alamun cututtukan da aka yi biris da su.
Mun san cewa jinyar marasa lafiya a yau na da mahimmanci, amma idan ba mu magance tsari da yanayin muhalli da ke haifar da wannan annoba ba, gobe ma za a fuskanci irin wannan cuta, har ma mafi munin ta yau.
Babban taron yanayi na Afirka da COP30 suna ba da damar da ba kasafai ake samun irin ta ba don sauya yanayinmu. Muna kira ga shugabanni, masu tattaunawa, da masu ba da taimako da su yarda cewa sauyin yanayi ba batun muhalli ba ne kawai; gaggawa ce ta lafiyar jama'a, kuma cututtukan na daga cikin alamun gargaɗin da hakan ke bayarwa na gaggawa.
Yaki da rikicin sauyin yanayi da gurbata lafiya
Mafita a bayyane take, amma suna buƙatar canji na asali a wajen duba al’amura. Dole ne mu wuce jiya wajen la'akari da waɗannan a matsayin "cututtukan talauci" kuma mu gane su a matsayin alamun girmamar rikicin-lafiya da yanayi.
1. Shigarta cututtukan kasashe masu zafi da aka yi birsi da su a cikin tsarin dabarun daidaita yanayi — Tsare-tsaren kula da yanayi na ƙasa, ya zama dole ne su yi la’akari da cututtuka masu alaka da sauyin yanayi, tare da sadaukar da kuɗi don sa ido, riga-kafi, da samar da magani.
2. Zuba hannun jari a cikin tsarin kiwon lafiya mai dore wa — Kayan aiki a yankuna masu fama da illolin sauyin yanayi su ma dole ne su sami ƙarfafuwa, ma'aikata, da albarkatu don magance rikice-rikice da yawa.
3. Haɗin gwiwa tsakanin bangarori- Lafiya, ruwa, tsaftar muhalli, da manufofin inganta yanayi, ya zama dole a daidaita su. Magunguna kadai ba za su iya dakatar da cututtukan da aka yi biris da su ba; suna buƙatar ruwa mai tsafta, ingantattun gidaje, da ingantattun kayan kula da lafiya.
Sauyin yanayi yana sake fasalin yadda cututtuka suke samuwa da yaduwa. Labaran da ke fitowa daga Marsabit, Wajir, da Old Fangak sun zama alamun gargaɗi ga lamarin da ke tafe idan ba mu ɗauki mataki ba.
Ga al'ummomin Gabashin Afirka masu rauni, cututtukan da aka yi biris da su a kasashe masu zafi suma ma'auni ne na shirye-shiryen mu na bai daya don tunkarar rikice-rikicen da ke tafe.
Ta hanyar cakuda matakin yaki da sauyin yanayi da ayyukan kiwon lafiyar jama'a, mayar da hankali kan cututtukan da suka fi saurin yaduwa saboda sauyin muhalli, za mu iya kiyaye ƙarin al'ummomi.
Lokaci ya yi da za a dauki mataki, kafin waɗannan boyayyun rikice-rikicen su ƙaru su zama bala'in da ba za a iya magance shi ba.
Idan muka gaza daukar matakan da suka kamata, za mu ƙara shaida barkewar annoba, da ƙarin wahalhalu ga mutane, da kuma nauyin jin kai a shekaru masu zuwa.
Mawallafin Endashaw Aderie, Babban Mai Ba da Shawara Kan Kiwon Lafiya ne a Kungiyar Likitocin Komai da Ruwanka wato Médecins Sans Frontières ko Doctors Without Borders (MSF)
Togaciya: Ba lallai ne ra’ayoyin da marubucin ya bayyana su zama sun yi daidai da ra'ayoyi da manufofin dab’i na TRT Afrika ba.