Ɓarayin daji sun sace mutum 43 daga wani masallaci da ke ƙauyen Gidan Turbe, a ƙaramar hukumar Tsafe na Jihar Zamfara da ke arewacin Nijeriya.
Kazalika rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 12 a ƙauyen Godai na ƙaramar hukumar Bukkuyum da ke Jihar a ranar Lahadi.
Lamuran dai sun faru ne a lokacin da shugabannin al’umma da wasu ‘yan bindiga a jihar Katsina mai maƙwabtaka suka ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan ta’addar.
Wasu masana na ganin idan ana son a magance matsalar tsaro a arewa maso yammacin Nijeriya, ya kamata gwamnatoci su yi sulhu da ‘yan bindiga a yankin, yayin da wasu ke ganin sulhu ba zai kawo ƙarshen matsalar ba.
Harin da aka kai kan masallacin na jihar Zamfara ya faru ne da kimanin ƙarfe 5:30 a lokacin da ake sallar asuba. Rohotanni sun ce ‘yan bindigar sun yi wa masallacin ƙawanya kuma suka yi awon gaba da masallata 43 inda suka nufi Dutsen Gahori da su.
Jiragen yaƙin Nijeriya sun yi luguden wuta a sansanonin ƴan ta'adda a Zamfara
Dutsen Gahori da ke ƙaramar hukumar Tsafe, yana cikin dokar daji da yake wani ɓangare na jihar Zamfara da wasu ɓangarori na jihar Kebbi har zuwa Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Rahotanni na cewa dajin wani wajen ɓuya ne na ƙungiyoyin ‘yan bindiga da ke aika-aika a sassan Zamfara da Sokoto da Kebbi.
Mazauna yankin sun yi zargin cewa yawancin sanannun shugabannin ‘yan bindiga ciki har da Bello Turji da Ado Aliero da Dogo Gide da Dan Isuhu da kuma Black, na da dabobinsu a kusa da Dutsen Gahori.
Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa harin da aka kai kan masallacin a jiya ya sa mutane sun ruɗe kuma sun yanke ƙauna.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun bar baburansu daga nesa kuma suka yi wa masallacin ƙawanya a hankali kafin su far wa masallatan.
Wannan harin ya jefa mutanen yankin cikin tashin hankali inda suka ce ƙauyukan da ke kusa da wurin na fama da ƙarin hare-haren ‘yan bindiga a kwanan nan.
“Mazauna wasu ƙauyuka kusa da Dutsen Gahori sun ƙaura daga gidajensu domin tsoron hari. A halin yanzu, ko ƙauyukan da suka ƙulla yarjejeniyar da ‘yan bindigar ma ba su tsira ba,” kamar yadda jaridar ta ambato Auwal Isa da ke zaune a Tsafe yana cewa.
“’Yan bindigar za su ƙulla yarjejeniya da wani ƙauye kuma su karɓi kuɗinsu, amma daga baya su kai musu hari. Wannan ita ce matsalar da muke fama da ita a jihar Zamfara,” in ji shi.