Ma’aikatan gidan radiyon gwamnatin Nijar, Rediyo-Télévision du Niger (RTN), sun fitar da sanarwar shiga yajin aiki na sa’o’i 48 domin nuna adawa da rashin tsaro da kuma neman a inganta yanayin aiki.
A cikin wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 10 ga Satumban 2025, wasu ƙungiyoyi da wakilan ma’aikatan kafar sun bayyana cewa ba su da wani zaɓi illa su tashi tsaye su ɗauki wannan mataki, suna masu kwatanta yanayin da su ke ciki da “abin takaici” wanda ya tura ma’aikata “cikin talauci da rashin tsaro.”
An dai shirya fara yajin aikin ne da tsakar daren ranar Talata 16 ga watan Satumba, sannan kuma a ƙare a ranar Laraba 17 ga watan Satumba da karfe 11:59 na dare.
Babban abin da suke buƙata shi ne a gaggauta aiwatar da ƙarin sabon albashin da kwamitin gudanarwa na RTN ya amince da shi a watan Disamban 2024 wanda kawo yanzu ba a aiwatar da shi ba balle a soma biya.
Kazalika ƙungiyoyin sun yi ƙorafi kan rashin amincewarsu da jinkirin biyan albashin ma’aikata tare da yin kira da a warware basussukan da ake bin su don rage wa iyalai matsalar kuɗaɗe.
Baya ga batun albashi, ma'aikatan sun koka kan barazanar rayuwa a RTN wanda a cewarsu ke cikin haɗari.
Suna neman a ƙara yawan tallafin da jihohi ke bayarwa don karfafa karfin aikin gidan rediyon a cikin abin da suka bayyana a matsayin "yakin yada labarai" wajen adawa da masu sukar ƙungiyar ƙawancen ƙasashen yankin Sahel.
Ba tare da isassun kuɗaɗe ba, sun yi gargadin cewa RTN ba za ta iya yin gogayya da kafofin yada labarai da shirye-shirye a yankin ba, ko kuma zama amintacciyar kafa ta muryar al’ummar Nijar.
Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da tashe-tashen hankula a ɓangaren yada labarai na Nijar, inda gidajen talabijin masu zaman kansu da dama ke fuskantar matsalar basussukan albashi na tsawon shekaru da kuma wadanda ke fafutukar ganin sun ci gaba da gudanar da aiki duk da hakan.
A yayin da ƙungiyoyin ke cewa a shirye suke don tattaunawa, sun dage kan cewa dole ne gwamnati ta yi gaggawar magance koke-kokensu.
Rashin yin hakan, a cewarsu na iya haifar da naƙasu sosai na rashin aiki a fagen watsa shirye-shirye da kuma yada labarai a fadin ƙasar—wanda ke nuna irin halin da aikin jarida ke ciki a Nijar.