AFIRKA
3 minti karatu
Al'ummar Ghana sun ƙaddamar da kamfe na neman soke Bikin Fina-Finan Isra'ila a Accra
Sun buƙaci hukumar gidan kallo na Silverbird da duk masu ɗaukar nauyin shirin da su janye, suna masu gargaɗin cewa rashin yin hakan zai haifar da ƙaurace wa bikin.
Al'ummar Ghana sun ƙaddamar da kamfe na neman soke Bikin Fina-Finan Isra'ila a Accra
Al'ummar Ghana sun kaddamar da kamfen soke bikin fina-finan Isra'ila a Accra saboda kisan gillar da ake yi a Gaza / TRT Afrika Hausa
5 awanni baya

Wata babbar gamayyar ƙungiyoyin ‘yan Ghana da ke ƙasashen waje ta kusan mutane 400 da wasu ƙungiyoyi, ta yi kira da a soke bikin nuna Fina-Finan Isra'ila da aka shirya gudanarwa a Silverbird Cinema, da ke Accra Mall a Ghana daga ranar 16 zuwa 20 ga Satumban 2025.

Matakin hakan na cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Litinin, inda masu fafutukar suka bayyana bikin a matsayin "wata farfaganda ta masu tsananin son kafa ƙasar Isra’ila" da nufin wanke "kisan ƙare-dangi da wariyar launin fata na Isra’ila" a yayin da ake ci gaba da tashin hankali a Gaza.

Sun buƙaci hukumar gidan kallo ta Silverbird da duk masu ɗaukar nauyin shirin da su janye, suna masu gargaɗin cewa rashin yin hakan zai haifar da ƙaurace wa bikin.

Gamayyar ƙungiyoyin sun yi zargin cewa, tarihin Ghana na gwagwarmayar ƙin jinin mulkin mallaka da haɗin- gwiwa da masu fafutukar ƙwato 'yancin kai ya sa bikin ya zama cin zarafi kai-tsaye ga ƙimar ƙasa.

"Ba za mu iya tsayawa muna kallo ba, yayin da ake bayyana kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa ta hanyar fasaha da al'adu.

“A ko yaushe Ghana na tsayawa a bangaren wadanda aka zalunta, kuma a yau dole ne mu tsaya tare da Falasdinu," in ji sanarwar.

Sanarwar ta ambato rahotannin ƙasashen duniya da kuma alkaluman Isra'ila, gamayyar kungiyoyin ta kuma zargi Isra'ila da sa ido kan mutuwar Falasdinawa sama da 200,000, kusan kashi 10 na al'ummar Gaza, ta hanyar ta da bama-bamai, da hare-hare da kuma yunwa.


'Yan adawar dai na samun goyon bayan fitattun jiga-jigan 'yan ƙasar Ghana, da suka hada da fitaccen ɗan jarida Kwesi Pratt Jnr., da tsohon kwamishinan CHRAJ Emile Short, da mai shirya fina-finai Nii Kwate Owoo, da wani malami Audrey Gadzekpo, da Dzodzi Tsikata, da kuma ɗan ƙungiyar kwadago Kwasi Adu-Amankwah, da mai zane Wanlov Kubolor, da mai fafutukar 'yancin yada labarai Kwame Karikari.


Sauran waɗanda suka sanya hannu kan sanarwar sun hada da; Oliver Barker-Vormawor na cibiyar ‘Democracy Hub’, da shugaban matasa Hardi Yakubu, Pan-Africanist Akyaaba Addi-Sebo, da kuma mai fafutukar ‘yancin mata Farfesa Akosua Adomako Ampofo.

Kazalika sun samu goyon bayan ƙungiyoyin kananan hukumomi, da na ƙwararru, da masu fasaha, da ɗalibai, da ƙungiyoyi addini, waɗanda ke wakiltar ɓangaren ƙungiyoyin farar hula na Ghana.

Haka kuma gamayyar ƙungiyoyin na ƙara matsawa kamfanoni da cibiyoyin da ke da alaƙa da bikin lamba, ciki har da SAF STL Amandi Foundation, da Kempinski Hotel, da Rolider, Sienna Services, da EON, da Jami'ar Media, Arts and Communication (UniMac).