WASANNI
2 minti karatu
PSG za ta nemi ɗauko Endrick daga Real Madrid
A Janairu mai zuwa PSG za ta gabatar da buƙatar ɗauko Endrick daga Real Madrid yayin da West Ham, Juventus, da Real Sociedad ke ƙoƙarin nemansa.
PSG za ta nemi ɗauko Endrick daga Real Madrid
Har yanzu Endrick matashi ne mai shekaru 19 kacal / Reuters
kwana ɗaya baya

Yayin da matashin ɗan wasan Real Madrid, Endrick ya gaza samun damar buga ko da minti ɗaya a wannan kakar, rahotanni na cewa ɗan wasan ya samu ƙungiyoyin masu sonsa.

Mai shekaru 19, Endrick ya rasa dama ƙarƙashin sabon kocin Madrid, Xabi Alonso inda sakonsa Arda Guler ya samu shiga jerin tawagar da ake yawan sakawa buga wasa.

A yanzu, ana raɗe-raɗin cewa ƙungiyoyi kamar Paris Saint-Germain ta Faransa, da West Ham ta Ingila da Real Sociedad ta Sifaniya, da Juventus ta Italiya sun fara shirya baza komarsu kan ɗan wasan.

Rahotannin na cewa ƙungiyoyin na jiran buɗe kasuwar cinikin ‘yan wasa ta baɗi a Janairu, domin gwada sa’arsu.

Waɗannan rahotannin za su yi wa ɗan wasan ɗan asalin Brazil daɗi saboda matsalar rashin buga wasa a gasannin La Liga balle ta Zakarun Turai.

Ya gaza buga yawancin wasannin ne saboda jinya da matsalolin kuzari, duk da an yi ta sanya shi a benci ba tare da an yi amfani da shi a wasa ba.

A kakar bara ƙarƙashin tsohon koci Carlo Ancelotti, Endrick ya buga wasanni 37, inda ya ci ƙwallaye bakwai.

Sai dai akwai rahotannin da cewa Real Madrid ba za ta sayar da ɗan wasan ba saboda yana da kwantiragi har zuwa 2030, duk da akwai saɗarar zaɓin sayar da shi.