KASUWANCI
1 minti karatu
Elon Musk na dab da zama mutum na farko da arzikinsa ya kai tiriliyan a duniya: rahoto
Shugaban kamfanin Tesla da SpaceX Elon Musk ya zama mutum na farko a duniya da arzikinsa ya kai dala biliyan 500.
Elon Musk na dab da zama mutum na farko da arzikinsa ya kai tiriliyan a duniya: rahoto
Elon Musk na dab da zama mutum na farko da arzikinsa ya kai Triliyan a duniya, a cewar wani rahoto / Reuters
11 awanni baya

Biloniya Elon Musk, wanda ya fi kowa arziki a duniya, na gab da zama mutum na farko wanda ya mallaki tiriliyan a duniya, a cewar mujallar Forbes.

Shugaban kamfanin Tesla da SpaceX ya zama mutum na farko da ya samu zunzurutun kuɗi har dala biliyan 500, yayin da hannun-jarin kamfaninsa na motoci masu aiki da lantarki ya farfaɗo, tare da wasu nasarorin da ya samu.

Yawan arzikin attajirin mai shekaru 54 ya kai dala biliyan 500.1 a ranar Laraba kafin ya koma dala biliyan 499.1, a cewar rahoton "Real-Time Billionaires" tracker da ke bibiyar manyan attajiran ƙasashen duniya.

A bayansa akwai shugaban kamfanin Oracle Larry Ellison wanda arzikinsa ya kai dala biliyan 350.7, sai kuma shugaban kamfanin Meta, Mark Zuckerberg, wanda ya mallaki dala biliyan 245.8 a cewar mujallar Forbes.

Bayan kammala karatunsa daga Jami’ar Pennysylvania bayan ya kori kansa daga Jami'ar Stanford, Musk ya samu miliyoyin kuɗinsa na farko lokacin da ya sayar da wani kamfaninsa na fasahar manhajojin intanet ga kamfanin kwamfuta na Amurka Compaq a kan fiye da dala miliyan 300 a shekarar 1999.