Abin da murabus ɗin Ministan Tsaron Nijeriya ke nufi da sauyin da zai haifar
NIJERIYA
3 minti karatu
Abin da murabus ɗin Ministan Tsaron Nijeriya ke nufi da sauyin da zai haifarAmma me wannan murabus ɗin ke nufi a fannin tsaron Nijeriya, kuma wane sauyi ake sa ran hakan zai haifar?
Badaru Abubakar / Reuters
2 Disamba 2025

‘Yan Nijeriya na ta bijiro da tambayoyi kan batun murabus din Ministan Tsaron Kasar, Mohammed Badaru Abubakar saboda dalilai na rashin lafiya, kamar yadda Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana.

Amma me wannan murabus ɗin ke nufi a fannin tsaron Nijeriya, kuma wane sauyi ake sa ran hakan zai haifar?

Badaru, wanda tsohon gwamnan Jihar Jigawa ne, da Shugaba Tinubu ya naɗa a kan muƙamin Ministan Tsaro a shekarar 2023, ya ajiye muƙaminsa ne a yayin da Nijeriya ke fama da ɗaya daga cikin ƙalubalen tsaro mafi girma tun bayan komawarta kan mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.

Ministan tsaron ya ajiye muƙaminsa ne a daidai lokacin da ‘yan fashin daji da mayaƙan Boko Haram suke ci gaba da cin karensu babu babbaka a arewa maso gabas da arewa maso yamma da kuma arewa ta tsakiyar Nijeriya.

Ya ajiye muƙaminsa ne makonni kaɗan bayan masu garkuwa da mutane sun sace ɗalibai aƙalla 25 daga wata makaranta a Jihar Kebbi da ke arewa maso yamma da kuma kusan ɗalibai 300 a Jihar Neja da ke arewa ta tsakiya.

Hakan ne ya tilasta wa gwamnatocin wasu jihohi rufe makarantu domin hana sace ƙarin ɗalibai. 

Kazalika hakan na faruwa ne makonni kaɗan bayan kisan da mayaƙan ISWAP suka yi wa wani Janar na sojin Nijeriya, wato Birgediya Janar Musa Uba.

Sannan a Jihar Kwara, ‘yan bindiga na ci gaba da ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare tare da sacewa da kuma kashe mutane, ciki har da hare-hare a kan wuraren ibada.

Tuni dai Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a fannin tsaron Nijeriya, tare da bayar da umarni a ɗauki ƙarin jami’an tsaro da sayen ƙarin kayan aiki domin shawo kan wannan lamari.
 Waɗannan jerin matsalolin tsaro na ƙamari ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin kai hari a Nijeriya kan zargin da ya yi cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar, lamarin da ya haifar da zazzafar muhawara tare da dugunzuma gwamnatin Tinubu, wadda ta tura mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan sha’anin tsaro Mallam Nuhu Ribadu Amurka domin ya tattauna da gwamnatin ƙasar kan yadda za su haɗa gwiwa domin shawo kan ƙalubalen tsaro.

Kuma wasu rahotanni na cewa korar Ministocin Tsaro na cikin manyan buƙatun Amurka ga gwamnatin Nijeriya, duk da yake sanarwar da Bayo Onanuga, kakakin shugaban Nijeriya, ya fitar ranar Litinin da maraice ta ce Badaru ya ajiye muƙaminsa ne saboda rashin lafiya.

Ko da yake a zamanin da Badaru ya jagoranci Ma’aikatar Tsaron Nijeriya an samu wasu gagaruman nasarori wadanda suka hada da kashe wasu manyan jagororin ‘yan bindiga da kama wasu shugabannnin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru.

Sai dai masana harkokin tsaro da masu sharhi kan lamuran yau da kullum suna ganin ya yi jan-ƙafa sosai game da yadda ya tunkari lamarin masu garkuwa da mutane, waɗanda duk da fitowar da suke yi a fili suna bayyana kansu, amma har ya sauka bai iya kama irin su Bello Turji ba.

Yanzu dai wasu bayanai sun nuna cewa Shugaba Tinubu yana shirin naɗa tsohon babban hafsan tsaron ƙasar Christopher Musa domin maye gurbin Badaru, matakin da ake gani yana iya kawo sauyi mai kyau a sha’anin tsaron ƙasar, kasancewarsa gogagge kuma mutumin da a baya ya taka rawar gani a fannin tsaron Nijeriya.

Tuni dai Shugaba Tinubu ya gana da Christopher Musa a fadar shugaban ƙasar da ke Abuja, abin da ake gani a matsayi wani mataki na kammala shirin naɗa shi a kan muƙamin ministan tsaron Nijeriya.