Daga Hafsa Abdiwahab Sheikh
Yaƙin Sudan ya rikide daga rikicin siyasa zuwa ɗaya daga cikin bala'o'in jinkai da na lafiyar jama'a mafi muni a duniya, tare da haifar da sakamakon da ya tsallaka iyakokinta.
Rikicin da ya ɓarke tsakanin Rundunar Sojin Sudan da Rundunar Taimakon Gaggawa ta RSF ya lalata muhimman ababen more rayuwa, ya gurgunta tsarin kiwon lafiya, ya kuma raba miliyoyin mutane da muhallansu.
Yayin da yunwa ke yaɗuwa, asibitoci suka lalace kuma dukkan al'ummomi suka gudu, hakan na bayyana karara cewa rikicin ya zama lamarin gaggawa na yanki.
Ana buƙatar tabbatar da ayyukan jinkai masu ƙarfi cikin gaggawa a tare da diflomasiyyar da Afirka ke jagoranta. Dole ne cibiyar siyasar duba kasar ta kasance a Afirka.
Wahalar da ɗan adam ke sha ta yi yawa. A cewar Rahoton Halin da ake ciki a Sudan na UNICEF na watan Janairun 2025, sama da mutane miliyan 30 - fiye da rabin al'ummar Sudan - yanzu suna buƙatar taimakon jinkai cikin gaggawa, kuma tsakanin miliyan 12 zuwa 14 sun rasa matsuguni, wanda hakan ya sa Sudan ta zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin gudun hijira a duniya.
Iyalai suna fakewa a gine-ginen da ba a kammala ba, makarantu cike da jama'a, da sansanonin da ba a kammala ba, galibi ba su da tsaftataccen ruwan sha, rashin tsaftar muhalli da kuma raguwar samun abinci.
Tare da kowace kididdiga akwai rugujewar rayuwa. Iyaye ba sa iya samun abinci, ga matasa da aka katse wa neman ilimi, da kuma al'ummomi da aka kwace musu kwanciyar hankali da suka daɗe tare da su.
Yanayin yunwa ya riga ya bayyana a sassan Kudancin Kordofan da Darfur, inda Al Fasher ke kan gaba a lamarin.
A cewar Mendy Hameda, tsohuwar Jakadiyar Zaman Lafiya ta Tarayyar Afirka a Gabashin Afirka, wadda a halin yanzu ke kula da kokarin da kungiyar agaji ta HRRDS ta Sudan (Hope Relief and Rehabilitation for Disability Support) ke yi, ana ci gaba da fafatawa da bama-bamai a ciki da kewayen Al Fasher.
Garin, wanda aka daɗe ana yi wa kawanya kuma yanzu haka yana ƙarƙashin ikon RSF, ya shaida kai hare-hare kan sansanonin 'yan gudun hijira, an lalata kasuwanni, an yanke kayan abinci, kuma wuraren kiwon lafiya sun zama tarkace.
Rahotannin sun ce dubban fararen hula sun tsere daga Al Fasher a tsakiyar tashin hankalin da ke ƙaruwa, suna yin gudun hijira da yawa, an lalata matsugunan 'yan gudun hijira, da kuma kusan rushewar ayyukan kiwon lafiya.
Rahotannin sun lura da cewa ma'aikatan agaji sun yi gargadin cewar yunwa na ƙara tsananta yayin da ayarin abinci ke gaza isa ga al'ummomin da ke cikin mawuyacin hali.
Har yanzu samun damar agajin jinkai na ɗaya daga cikin ƙalubale mafi girma. Ana kai wa ayarin agajin hari akai-akai, ana hana su wuce wa, ko kuma ana tare musu hanya.
Ko da lokacin da masu ba da gudunmawa suka saki kuɗaɗe, yawanci taimakon ba ya iya isa ga mutanen da suka fi buƙatarsa. Ƙungiyoyin agaji sun bayyana cewa an katse da tare hanyoyin isa ga dukkan al'ummomi na tsawon makonni.
A wurare da dama, ƙungiyoyin sa kai, masu horar da likitoci, da ƙungiyoyin fararen hula na gida suna zama masu bayar da agaji na farko na gudanar da ayyuka ba tare da kayan aiki ba. Jarumtakarsu abin mamaki ce, amma ikon da suke da shi na da iyaka.
A cikin wannan yanayi ne diflomasiyya da Afirka ke jagoranta ba wai kawai ta zama maim muhimmanci ba, ta zama wajibi.
Hukumomin yanki kamar Tarayyar Afirka (AU) da IGAD suna da haƙƙi, kusanci, da fahimtar mahallin da ake buƙata don yin sulhu yadda ya kamata.
Duk da cewa shirye-shiryen da suka gabata sun haifar da dakatar da ayyukan jinkai na ɗan lokaci, rikicin da ke ƙara ta’azzara na buƙatar ƙoƙarin siyasa mai tsari.
Kuma mafi muhimmanci shi ne, idan aka yi la'akari da al'ummar duniya da suka nuna halin ko in kula ko suka nuna ba sa son shiga tsakani yadda ya dace, to mafi girman nauyin na kan shugabannin Afirka.
Yayin da 'yan gudun hijira, wadanda aka raba da matsugunansu da fararen hula da aka ritsa da su a Al Fasher ke fuskantar yunwa da tashin hankali, nahiyar ba za ta iya jiran masu ruwa da tsaki na waje waɗanda abubuwan da suka fi ba wa muhimmanci ke wani wujen na daban ba.
Dole ne cibiyoyin Afirka su yi aiki da gaggawa yanzu. Duk da cewa AU da IGAD sun yi ƙoƙarin mayar da martani, ƙoƙarinsu ya rarrabu, kuma sau da yawa yana mamaye da ra’ayoyin diflomasiyya masu karo da juna.
AU ta fitar da sanarwa kuma ta yi kira ga tarurruka, amma ba ta kafa tsarin sulhu mai ɗorewa ba, wanda ke da ikon da zai iya tilasta wa SAF da RSF su tattauna da juna ko tabbatar da samun damar ayyukan jinkai.
Wannan gibin yana nuna ƙarancin hanyoyin aiwatar da aiki da kuma dogaro kan shirye-shiryen diflomasiyya na waje, kamar kasashe ‘yan hudu na ‘Quartet’ na Duniya (wanda ya ƙunshi Saudiyya, Amurka, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Masar), waɗanda ba su samar da mafita ba har yanzu.
Ta hanyar fahimtar yanayin siyasa da zamantakewa na Sudan, hanyar neman mafiya daga kasashen Afirka ba wai ta je ka na yi ka ba ce. a’a dole ce.
Yana buƙatar tsarin haɗin gwiwa wanda aka gina a kan ginshiƙai huɗu masu mahimmanci:
1) Tawagar sulhu ta AU-IGAD wacce wakili ɗaya mai iko ke jagoranta tare da umarni bayyananne
2) Aikin sa ido da tabbatar da bin diddigin tsagaita wuta na yanki da kuma tabbatar da hanyoyin kai kayan jinkai
3) Rundunar agaji ta nahiyar Afirka da ke aiki kai tsaye tare da ƙungiyoyin farar hula na Sudan da wadanda ke kan gaba wajen tallafa wa jama’a.
4) Taro na yau da kullun na gaskiya ga cibiyoyin Afirka da jama'a don ci gaba da ɗaukar nauyin da ya rataya a wuyansu.
Dole ne Ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, musamman Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, su ƙarfafa shugabancin Afirka.
Dole ne masu ruwa da tsaki na duniya su bayar da tallafin dabaru don isar da agaji, ci gaba da samar da kuɗaɗen agaji da matsin lamba na diflomasiyya ga ɓangarorin da ke yaƙi.
Dole ne al'ummar duniya su fahimci cewa rugujewar Sudan zai haifar da gudun hijira ala tilas, zai wargaza iyakoki da kuma ƙara tsananta rashin tsaro a duk faɗin yankin da ke fama da rikici da illolin sauyin yanayi.
Hanyar da za a bi don ci gaba tana buƙatar matakai na zahiri. Ya kamata a tattauna hanyoyin jinkai, a aiwatar da su, kuma a sa ido a kansu, tare da tabbatar da kare fararen hula ba tare da wasu sharudda ba.
Dole ne a kawar da sojoji daga wuraren asbitoci, sannan a amince da su a matsayin wuraren agaji masu kariya.
Dole ne a sake buɗe hanyoyin samar da kayayyaki masu mahimmanci tare da sa ido a fili don hana karkatar da taimakon. Dole ne a bayar da fifiko ga shirye-shiryen abinci mai gina jiki na gaggawa da gangamin allurar rigakafi mai yawa, musamman ga yara da suka riga suka nuna alamun rashin abinci mai gina jiki a jikinsu.
Rashin ɗaukar mataki zai haifar da mummunan sakamako. Hukumomin agaji sun yi gargaɗi game da iyalai da ke ba sa cin abinci na tsawon kwanaki, suna tafiya nesa don samun ruwa mara kyau, da kuma sayar da kayansu da suka rage don su rayu.
Rushewar tattalin arziki mai zurfi a Sudan zai kawo cikas ga yankin da ke faɗaɗa: ƙara yawan hijira, raunata tsaron kan iyaka, barazanar hanyoyin kasuwanci da ƙara ta'azzara rikici a faɗin yankin Afirka da Sahel.
Kwanciyar hankali a Sudan ba wai kawai wani muhimmin abu ne na jinkai - a’a abu ne mai muhimmanci da ya zama dole a samar da shi.
Sudan na cikin mawuyacin hali. Idan ba a samu matsin lamba na diflomasiyya nan take ba, samun damar jinkai mai dore wa, da kuma kyakkyawan haɗin gwiwa da Afirka ke jagoranta, ƙasar za ta ci gaba da fuskantar hatsarin rasa dukkan al’umarta saboda yunwa, cututtuka, da tashin hankali.
Dole ne nahiyar ta yi jagoranci, kuma abokan hulɗa na duniya su goyi baya - domin dole ne cibiyar siyasar warware rikicin Sudan ta kasance a Afirka.
Miliyoyin 'yan Sudan suna jiran shugabanci wanda ya fahimci gaggawar wannan lokacin kuma ya yi aiki da ƙudurin da suke buƙata.
Marubuciyar, Hafsa Abdiwahab Sheikh 'yar jarida ce mai zaman kanta kuma mai bincike da ke mayar da hankali kan siyasar Gabashin Afirka.
Togaciya: Ba lallai ne ra’ayin da marubuciyar ta bayyana ya zama ya yi daidai da ra’ayoyin dab’i na TRT Afrika ba.













