KASUWANCI
2 minti karatu
Dangote zai mai da ma'aikatan Matatar Mai da aka kora daga aiki - Ma'aikatar Ƙwadagon Nijeriya
Ma’aikatar Ƙwadago ta ce za a dawo da ma’aikatan da aka kora bakin aiki a dukkan sassan kamfanin Dangote ba tare da tauye wani kudi da za a biya su ba.
Dangote zai mai da ma'aikatan Matatar Mai da aka kora daga aiki - Ma'aikatar Ƙwadagon Nijeriya
Ma'aikatan a gaban matatar mai ta Dangote da ke binin Legas na Nijeriya. / Reuters
1 Oktoba 2025

Kungiyar Ma’aikatan Mai a Nijeriya ta amince ta janye yajin aikin da ta tsunduma bayan wata ganawa da ta yi da mahukuntan kamfanin man Dangote da jami’an gwamnati, kamar yadda Ma’aikatar Ƙwadago ta kasar ta bayyana.

An tsunduma yajin aikin ne bayan da Matatar Mai ta Dangote - wadda ita ce mafi girma a nahiyar Afirka mai karfin tace danyen mai ganga 650,000 a kowace rana - ta kori ma'aikatan kungiyar fiye da 800.

Rikicin ya yi barazana ga samar da man fetur da kasuwanci a fadin yammacin Afirka.

Ma’aikatar Ƙwadagon ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar bayan wani zaman sulhu tsakanin kungiyar ta PENGASSAN da kamfanin mai na Dangote, inda ta ce za a dawo da ma’aikatan da aka kora aiki a wasu sassan rukunin Dangote ba tare da asarar albashinsu ba.

Ministan Ƙwadagon ya shaida wa taron cewa kafa kungiya hakki ne na ma’aikata don haka ya kamata a mutunta matakin.

Sanarwar ta kara da cewa "PENGASSAN ta amince ta fara shirin janye yajin aikin."

An kori ma’aikatan matatar mai na Dangote a ranar Alhamis saboda kafa kungiya, inji PENGASSAN a ranar Juma’a.

A lokacin korar jami’an matatar man Dangote sun bayyana cewa korar ma’aikatan wani bangare ne na sake fasalin ma’aikatan tare da zargin wadanda abin ya shafa da yin zagon kasa.