Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Yusuf Tuggar ya ce bai kamata ƙasashe masu arziki su dinga ɗaukar kasuwanci da Afrika a matsayin wasan ɗiban ma’adanai inda suke diban albarkatun kasa ba, maimakon haka kamata ya yi su kulla alakar da ta ginu bisa mutunta juna da bukatar ci gaban Afirka.
Yusuf Tuggar ya kuma ce Nijeriya kasa mafi yawan al'umma a Afirka, kuma mai fitar da danyen man fetur, harajin Amurka bai shafe ta sosai ba idan aka kwatanta da sauran kasashe saboda girman ta da abokan mu’amala da yawa da take da su.
"Yana da matukar muhimmanci wajen tunkarar Afirka ga yankin arewacin duniya da kuma kasashen da suka ci gaba kar su yi amfani da tunanin mayar da Afirka wajen dian ma’adanai."
Tuggar ya fada a ranar Laraba yayin wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Reuters a taron kolin Gulf na NEXT a Abu Dhabi.
"Wani lokaci yana kama da wasan diban ma’adanai: Akwai mai, akwai iskar gas, akwai ma'adanai masu mahimmanci, ƙasa da ba a ko’ina ake samun irin ta ba. Mun sanya kudi kadan a cikin wannan, muna saka hannun jari a wannan waje. A'a, ba haka abin yake ba."
"Ya kamata mu’amalar da zama bisa doron girmama juma, manufofin bai daya da gaskiyar cewa Afirka na bukatar ci gaba. Idan ba ta ci gaba ba, za mu ci gaba da fama da gudun hijira ba bisa ka’ida ba, tare da dukkan wadannan kalubale.” in ji shi
Shahararren wasan bidiyo na hakar ma’adanai ya ƙunshi 'yan wasa da ke bincika duniyar 3D da aka yi da wasu dunkulallun duwatsu wadanda za su iya haƙar ma'adinai a cikin su, kayan sana’a da gina gine-gine.
Kasashen Afirka masu arzikin albarkatun kasa, irin su Najeriya mai man fetur da iskar gas ko kuma Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango da ke da ma'adanai masu mahimmanci, sun dade suna fafutuka wajen habaka tattalin arzikinsu da rage dogaron da suke yi na fitar da albarkatun kasa zuwa kasashen waje.
Da aka tambaye shi game da manufofin shugaban Amurka Donald Trump kan haraji, wanda ke sanya harajin kashi 15 cikin 100 kan kayayyaki daga Najeriya da suka hada da man fetur da iskar gas, Tuggar ya ce Najeriya na da wasu damarmaki da za su taimaka mata wajen jure wa wannan matsala.
"Mu kasa ce babba mai yawan mutane miliyan 230, don haka muna da babbar kasuwa ta cikin gida," in ji shi. "Hakan kuma yana nufin muna da tarin basira fiye da sauran ƙasashe."
“Kuma ba shakka za mu iya yin kasuwanci da wasu kasashe wanda shi ne abin da gwamnatin Tinubu ke kokarin jaddadawa – ‘yancin cin gashin kai mai nasibi,” in ji shi, yayin da yake magana kan Shugaba Bola Tinubu.
"Dangantakarmu ba ta dogara ne kan akida ba, tana dogara ne kan manufa, tun daga kan muradun kasa, don haka muna yin ciniki da Amurka, muna yin ciniki da China, muna ciniki da Brazil, muna ciniki da Indiaa."
"Kuma ba lallai ne mu mayar da hankali ga wani bangare ko wani tilo ba, musamman a cikin duniyar yau mai rarrabuwar kawuna."