Sakataren Ma’aikatar Yaƙi na Amurka, Pete Hegseth, ya ce ma’aikatarsa na shirin ɗaukar matakin soja idan gwamnatin Nijeriya ta gaza kawo ƙarshen “kashe-kashen Kiristoci marasa laifi” a ƙasar.
Hegseth ya yi wannan magana ne a ranar Asabar, yana mayar da martani ga wani saƙo da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a Truth Social, inda ya zargi gwamnatin Nijeriya da yin shiru kan hare-haren da ake kai wa Kiristoci.
“Ina gargadi: “Muddin gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan-take, kuma mai yiwuwa za ta shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da 'yan ta'adda masu kaifin kishin Musulinci waɗanda ke yin wannan ta’asa,” in ji Trump.
Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa: ”Ina bayar da umarni ga Ma'aikatar Yaƙinmu ta yi shiri domin yiwuwar ɗaukar mataki. Idan muka kai hari, zai kasance mai sauri da kaifi kuma daɗi, kamar dai yadda ‘yan ta’adda suke kai hari kan ababen ƙaunarmu Kiristoci.”
Hegseth ya hanzarta maimaita saƙon Trump a dandalin sada zumunta na X.
“Na’am, ranka ya daɗe. Kashe Kiristoci marasa laifi a Nijeriya — da ko’ina — dole ne ya ƙare nan da nan,” in ji Hegseth.
“Ma’aikatar Yaƙi tana shirin ɗaukar mataki. Ko dai gwamnatin Nijeriya ta kare Kiristoci, ko kuma mu kashe Musulmai ‘yan ta’adda da ke aikata waɗannan manyan laifuka.”
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake yi wa Kiristoci kisan gilla.
Ya ɗora alhakin “kashe Kiristoci da yawa” a kan Musulmai masu tsattsauran ra’ayi.
Shugaba Bola Tinubu ya ƙi amincewa da wannan lakabi da Trump ya bai wa Nijeriya, inda ya ce duk wani bayani da ke nuna cewa Nijeriya ƙasa ce mai fama da tsatsauran ra’ayin addini, ba ya nuna ainihin gaskiyar abin da ke faruwa a ƙasa, kuma ba ya la’akari da ƙoƙarin gwamnati wajen tabbatar da ‘yancin yin addini da ra’ayi ga kowa da kowa.









