Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da 'yan tawayen M23 sun rattaɓa hannu kan wata yarjejeniyar da nufin samar da zaman lafiya da kuma kawo ƙarshen yaƙi.
An sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar Asabar wadda wakilai daga ɓangarorin biyu suka saka hannu wa a wani taro a babban birnin Qatar, Doha.
Qatar tare da Amurka da Tarayyar Afirka sun shafe watanni suna gudanar da jerin tattaunawa don kawo ƙarshen rikici a gabashin DRC mai arzikin ma'adinai, inda M23 ta ƙwace manyan birane.
‘Yan tawayen na M23 a wani mataki da suka ɗauka na baya-bayan nan da goyon bayan maƙwabciyar Kongo wato Rwanda, sun ƙwace birnin Goma a watan Janairu, birni mafi girma a gabashin DRC, inda suka ci gaba da ƙwace wasu garuruwa a lardunan Kivu ta Arewa da Kivu ta Kudu.
Tun bayan sake ɗaukar makami a ƙarshen 2021, rukunin M23 ya ƙwace manyan yankuna a gabashin DRC tare da tallafin Rwanda, abin da ya haddasa mummunan rikicin jinƙai.
Rwanda ta musanta cewa tana tallafa wa M23
A yayin bikin ƙulla yarjejeniyar a Doha, babban mai sulhu na Qatar, Mohammed Al-Khulaifi, ya kira yarjejeniyar "ta tarihi", yana mai cewa masu shiga tsakani za su ci gaba da ƙoƙari don tabbatar da zaman lafiya a fagen.
Dubban mutane sun mutu a wani farmaki da M23 ta kai a watan Janairu da Fabrairu, wanda a ciki kungiyar ta kwace manyan biranen lardi na Goma da Bukavu.
Yarjejeniyar watan Yuli da aka sanya wa hannu a Doha ta biyo bayan wata ta daban, yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatocin DRC da Rwanda da aka rattaɓa wa a Washington a watan Yuni.
Qatar ta karɓi baƙuncin tattaunawa daban-daban tsakanin gwamnatin DRC da M23 tun watan Afrilu.
A watan Oktoba, sun cim ma yarjejeniya kan yadda za a sa ido a kan tsagaita wuta

















