KASUWANCI
2 minti karatu
Kamfanin simintin Dangote ya fara aiki a ƙasar Ivory Coast
Rahotanni sun ce kamfanin da ke zaune a kan filin da ya kai kadada 50 yana iya samar da tan miliyan uku na siminti a ko wane shekara, lamarin da ya mayar da shi masana’anta mafi girma na kamfanin a wajen Nijeriya.
Kamfanin simintin Dangote ya fara aiki a ƙasar Ivory Coast
Ana hasashen masana'antar za ta samar da ayyukanyi sama da 1,000 / Dangote/X
13 Oktoba 2025

Kamfanin simintin Dangote ya fara aiki a hukumance a Attingué, kimanin kilomita 30 daga birnin Abidjan na ƙasar Ivory Coast.

Wata sanarwa da rukunin kamfanonin Dangote ya fitar ranar Lahadi ta ce ranar Laraba ne babban daraktan kamfanin simintin Dangote na ƙasar Ivory Coast, Serge Gbotta, ya bayyana haka a otel ɗin Novotel Abidjan-Marcory.

Rahotanni sun ce kamfanin da ke zaune a kan filin da ya kai kadada 50 yana iya samar da tan miliyan uku na siminti a ko wace shekara, lamarin da ya mayar da shi masana’anta mafi girma ta kamfanin a wajen Nijeriya.

“Wannan muhimmin aikin, wanda jarin da aka zuba a kansa ya kai kuɗin CFA francs biliyan 100 ya tabbatar da manufar Aliko Dangote ta gina Afirka mai dogaro da kanta wadda ke da ƙarancin dogaro kan kayayyakin da ake shigarwa daga ƙasashen waje da kuma ikon iya sauya ma’adananta zuwa kayayyakin da aka ƙera masu inganci irin na ko ina a duniya,” in ji sanarwar.

“Da wannan  masana’antar, Ivory Coast ta zama ƙasar Afirka ta 11 wadda ke da kamfanin simintin Dangote. Kamfanin wanda ke iya samar da tan miliyan 55 na siminti a ko wace shekara cikin nahiyar, yana son ya ba da gudunmawa wajen gina ababen more rayuwa na ƙasar Ivory Coast da kuma biyan buƙatun kayayyakin gine-gine da ke ƙaruwa sakamakon girman birane cikin sauri da manyan gine-gine da ake yi a ƙasar,” in ji ta.

“Hasashe ya nuna cewa masana’antar Attingué za ta iya samar da ayyuka fiye 1,000 kai-tsaye ko a kaikaice. Wannan wani muhimmin abu ne ga matasa a Ivory Coast, da ma yanayin [harkokin] ƙananan masana’antu – masu ababen hawa da gine-gine da dillalai da masu kawo kaya da ma ‘yan kwangila,” in ji sanarwar.

A wajen ƙaddamar da masana’antar, shugaban kamfanin simintin Dangote a Ivory Coast ya ce, “Burinmu a bayyane yake: mu samar wa ‘yan Ivory Coast siminti mai inganci irin na ƙasashen duniya a farashi mai sauƙi. Masana’antar Attingué ba masana’anta ba ce kawai; wata alama ce ta aminci ga makomar Ivory Coast da kuma jajircewa kan ci-gaba mai ɗorewa da kuma al’umomin ƙasar.”