| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Cristiano Ronaldo zai fito a fim ɗin "Fast & Furious"
Jarumin sanannen fim ɗin hatsabibanci na "Fast & Furious", Tyrese Gibson ya ba da hasken cewa gwarzon ɗanwasan ƙwallo Cristiano Ronaldo zai fito a fim ɗin da za a saki nan gaba.
Cristiano Ronaldo zai fito a fim ɗin "Fast & Furious"
Cristiano Ronaldo yana shirye-shiryen fara rayuwa bayan yin ritaya daga ƙwallo. / AP
18 Disamba 2025

Shahararren jarumin fina-finan Amurka, Tyrese Gibson ya yi ishara da cewa gwarzon ɗanƙwallon duniya, Cristiano Ronaldo zai fito a mashahurin fin ɗin nan na Fast & Furious.

Gibson ya wallafa hoto a shafinsa na soshiyal midiya, wanda da ya nuna sanannun jaruman fim ɗin a wani waje da ya yi kama da wurin da ake shirya fim ɗin kashi na gaba.

Hoton ya nuna jaruman fim ɗin kamar Vin Diesel da Dwayne “The Rock” Johnson tare da Ronaldo. Gibson ya rubuta taken cewa, “Barka da zuwa cikin dangi! @cristiano Rawar duniya za ta shiga wani mataki”.

Fim ɗin dai ya yi suna wajen nuna motoci da sauran ababen hawa da jarumai kan tuƙa suna tsere, kuma ya ƙunshi jarumai da suka yi suna a masana’antar fina-finan Hollywood ta Amurka.

Tun a baya ne Vin Diesel ya janyo raɗe-raɗin fitowar Ronaldo lokacin da ya wallafa a Instagram cewa masu shoirya fim ɗin sun “rubuta rol” musamman ga ɗanwasan mai farin jini.

Kashin farko na fim ɗin ya fara fita ne a 2001, kuma ana dakon fitowar kashi na gaba wanda shi ne karo na goma sha ɗaya, a 2027.

A 2013, wani jarumin fim ɗin mai suna Paul Walker ya mutu sakamakon hatsarin mota, kuma an daɗe ana hasashen za a samu wanda zai hau rol din marigayin.

Tauraruwar Ronaldo

Labarin cewa akwai yiwuwar ɗanwasan ɗan asalin Portugal, Cristiano Ronaldo ya fito a fim ya ja hankalin masoya ɗanwasan.

Bayan cika shekara 40 a bana, yana shirye-shiryen yin ritaya daga ƙwallo, kuma ana ganin tauraruwarsa za ta ci gaba da haskawa a wasu fannonin nishaɗantarwa.

A Afrilun shekarar nan ta 2025, Ronaldo ya sanar da kafa sutudiyon shirya fina-finai tare da haɗin-gwiwar daraktan fin ɗan Birtaniya, Matthew Vaughn.

An fassara hakan a matsayin wata alama mai nuna aniyar Ronaldo ta shiga harkar fim.

Zuwa yanzu dai ɗanwasan na ci gaba da taka leda a ƙungiyar Al-Nassr ta Saudiyya, kuma zai buga wa ƙasarsa Portugal gasar Kofin Duniya na 2026 a baɗi.